Aikin Zirga-Zirgar Jiragen Sama Ta Fasinja Ta Sin Ya Bunkasa Zuwa Sabon Matsayi
Published: 23rd, July 2025 GMT
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.
Cikin taron aiki da hukumar zirga-zirgar jigaren sama ta fasinja ta kira a jiyan, shugaban hukumar Song Zhiyong ya bayyana cewa, an gudanar da aikin tsaro yadda ya kamata, ganin aikin zirga-zirgar jiragen sama ya karu da kaso 5.6 bisa dari cikin rabin farkon bana, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.
Haka zalika, a rabin farkon na bana, tsawon lokacin zirga-zirgar jiragen sama na gama gari ya kai awoyi dubu 570, kana, yawan jiragen sama marasa matuki da jama’ar kasa suka yi rajista ya kai miliyan 2 da dubu 726. Lamarin da ya nuna cewa, harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta gama gari, da tattalin arzikin jiragen saman dake zirga-zirga kusa da doron kasa, suna bunkasuwa bisa tsari. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: zirga zirgar jiragen sama ta ya karu da kaso
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
Yau Talata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”.
Yayin taron, jami’in kungiyar nakasassu ta Sin ya bayyana cewa, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, an kiyaye hakki da moriyar nakasassu na kasar yadda ya kamata.
A halin yanzu, kasar tana da dokoki da ka’idoji sama da 180 da suka shafi kare nakasassu, ciki har da “Dokar gina muhalli marar shinge”, kuma akwai dokoki da ka’idoji 41 na kasa da suka kara tanade-tanade don kare hakkoki da muradun nakasassu a lokacin tsarawa da gyara abubuwan da suka shafi muhalli.
Bugu da kari, a lokacin aiwatar da “shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”, an aiwatar da wani shirin na tsawon shekaru uku (2022-2024) domin taimakawa nakasassu wajen samun ayyukan yi, inda yawan nakasassun dake samun ayyukan yi ya karu akai-akai. Ban da haka kuma, a cikin wannan wa’adi, nakasassu fiye da miliyan 9 ne aka ba su ayyukan yi a fadin kasar, kuma adadin sabbin ayyukan yi na nakasassu a birane da kauyuka ya kai miliyan 2.31. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp