An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano
Published: 23rd, July 2025 GMT
Wasu fusatattun matasa sun banka wa wani babur din Adaidaita Sahu da ake zargin na barayin waya ne wuta a unguwar Sharada da ke cikin birnin Kano da safiyar Laraba.
Barayin da ake zargi dai sun shiga wata makaranta mai zaman kanta ne da ke Sharada mai suna Al-Abbas College, inda suka ce sun zo nema wasu yaransu gurbin karatu ne amma suka sace wayar shugaban makarantar.
Da yake zantawa da Aminiya, daya daga cikin malaman makarantar, Malam Sunusi Hamisu, da ya shaida yadda lamarin ya faru, ya ce, “Matasa ne guda biyu da suka ce sun zo neman gurbin karatu na yara guda biyu a aji biyu da aji uku na Firamare saboda sun ce sun canza gari ne sun dawo Kano daga Kaduna.
Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta“To ni ne ma na raka su ofishin shugabar makaranta, sai ta ce a kai su ofishin mai makarantar, inda ya yi musu lissafin kudin rajista da na fom, sai suka ce ya dauko musu. To ya tashi zai dauko musu sai wayarsa ta fado, inda nan take suka dauke ta suka gudu.
“Fitarsu ke da wuya sai ya duba ya ga bai ga wayarsa ba, sai ya bi su da gudu ya karbi wayar, a lokacin har sun riga sun cire ta daga cikin gidanta sun cire layin sun kuma kashe ta.
“Da ya biyo su sai suka gudu suka shiga Adaidaita Sahun da suka zo da shi wanda ya tsaya a bakin titi yana jiran su. Nan take sai suka gudu a cikin babur din sai malamin ya fada wa mutane ga barayin waya, inda mutane suka yi kukan kura suka kama su.
“Da direban babur din ya ga an cim musu za a kama su, sai ya gudu ya bar babur din da barayin biyu a ciki, wadanda su kuma aka kama su,” in ji Malam Sunusi.
Ya ce bayan kama barayin ne aka mika wa ’yan sanda su, babur din kuma aka shigar da shi cikin makarantar.
To sai dai ya ce bayan an shigar da babur din ne sai matasan unguwa suka yi zuga suna barazanar balla kofar shiga makarantar idan ba a ba su babur sun kona ba, wanda ala tilas aka ba su suka fitar da shi suka banka masa wuta a bakin titi.
Shi ma wani mutum da abin ya faru a kan idanunsa mai suna Abdullahi Musa, ya ce an lakada wa barayin dukan tsiya kafin an damka su ga ’yan sanda sannan a kona babur din nasu.
“Mun riga mun yanke shawarar duk lokacin da muka kama babur din barayi sai mun kone shi, ta haka ne za su shiga taitayinsu,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sharada
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar Washington Post Ta Ce; Yeman Ta Gurguta Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Isra’ila
Jaridar Washington Post ta bayyana cewa: Cikakken gurgunta tashar jiragen ruwa na Eilat da ke haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana tasirin ikon Yemen
Jaridar Washington Post ta Amurka ta tabbatar da cewa rufe tashar jiragen ruwa ta Umm al-Rashrash na karshe ya nuna tasiri da karfin hare-haren Yemen ke da shi.
A cikin wani babban rahoto da aka buga a ranar Litinin, jaridar ta lura cewa, bayanan da jami’an mamayar Isra’ila suka yi game da gurguncewar da tashar jiragen ruwa ta yi, sun bayyana a fili “cikakkiyar nasarar da ‘yan Yemen suka yi.”
Jaridar ta yi hasashen cewa: Kasar Yemen za ta iya aiwatar da sauye-sauyen dabarun yaki a yankin, inda ta yi nazari kan wasu ayyukan sojojin ruwan kasar Yemen da suka tilastawa jiragen yakin Amurka gudu daga yankin, tare da sanadin nutsewar jiragen ruwa da dama da suka sabawa umarninsu, lamarin da ya sa sojojin Amurka da na yammacin Turai suka kasa yin komai a kansu.
Jaridar ta lura cewa ayyukan Yemen sun sanya tasirin su tun farkon harin da suka kai ga jirgin ruwan jigilar gwamnatin mamayar Isra’ila a karshen shekara ta 2023, da ya tabbatar da cewa ayyukan sun ragu da kashi 90 cikin 100 cikin kankanin lokaci, kafin tashar ta kai ga barin aiki kwata-kwata.