Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
Published: 23rd, July 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya nuna cewa; Jami’an gwamnatin Obama sun murguda bayanai game da katsalandan din Rasha a zaben Amurka na shekara ta 2016.
Kalaman na Trump sun zo ne yayin wani taron manema labarai a ofishin Oval, wanda shugaban kasar Philippines Ferdinand Marcos ya halarta. Yana cewa:”Bisa ga abin da ya karanta…tsohon shugaba Obama ne ya fara wannan badakalar,” ya kara da cewa Obama shi ne “shugaba” na abin da ya bayyana a matsayin “gungun maciya amana.”
An karfafa wadannan zarge-zarge ne bayan da Daraktar hukumar leken asirin kasar Tulsi Gabbard ta aike da masu gabatar da kara ga ma’aikatar shari’a dangane da wani rahoto da aka fitar a ranar Juma’ar da ta gabata da ke tabbatar da cewa jami’an gwamnatin Obama na da hannu wajen kirkirar bayanan sirri da nufin share fagen juyin mulki na tsawon shekara daya kan shugaba Trump.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA