Karfin Lantarki Da Tashoshi Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Ke Samarwa A Sin Ya Kai Kilowatt Biliyan 2
Published: 27th, March 2025 GMT
A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu.
Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.
Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da lantarki lantarki da
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan
Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari.
Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka zarce ‘yan ciranin gargajiya na wasu kasashe kamar ‘yan Siriya da Falasdinawa.