2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed
Published: 23rd, July 2025 GMT
Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi wa Peter Obi, takarar mataimaki a zaɓen 2023, ya ce yana goyon bayan Obi idan yana so ya sake yin takara a 2027, ko da ba tare da shi ba.
Peter Obi da Datti sun tsaya takara tare a 2023 sai dai sun ƙare a na uku.
NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule LamidoShugaba Bola Tinubu ne ya lashe zaɓen.
Datti, ya ce Obi yana da ’yancin sake tsayawa takara a ƙarƙashin LP.
Ya kuma ce ba dole ne sai Obi ya yi haɗin gwiwa da shi ba.
“Peter Obi mutum ne da nake girmamawa ƙwarai. Yana da damar sake fitowa takara a 2027, ko da ba tare da ni ba,” in ji Datti a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
Datti, wa ds tsohon Sanata ne, ya ce Najeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya da za su iya kawo ci gaba, ba masu alƙawuran ƙarya ba.
“Muna cikin wani yanayi mai muhimmanci. ’Yan Najeriya na buƙatar aiki ba uzuri ba. Muna buƙatar shugabanni masu cika alƙawari da gyara ƙasa,” in ji shi.
Game da shigar Peter Obi a wata haɗakar siyasa a jam’iyyar ADC, Datti ya ce hakan ba laifi ba ne.
“Haɗin gwiwa a siyasa ba cin amanar jam’iyya ba ne. Hakan al’ada ce a siyasa, inda mutane da jam’iyyu ke haɗuwa don cimma buri ɗaya.
“Ni ma na halarci wasu daga cikin tarukan. Ba wani abu ba ne da ya saɓa wa doka ko tsarin jam’iyya,” in ji shi.
Ya ce wannan haɗin gwiwar na da nufin samar wa ’yan Najeriya zaɓi mai kyau duba da halin da ake ciki.
Game da batun karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, Datti, ya ce kamata ya yi shugabancin ƙasa ya koma Kudu a 2027.
Ya ce wannan ba lissafin siyasa ba ne, amma manufar adalci da haɗin kai a ƙasa mai yawan ƙabilu kamar Najeriya ne.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa Siyasa Takara Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria