Aminiya:
2025-07-23@21:43:53 GMT

Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa

Published: 23rd, July 2025 GMT

Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa.

Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu.

An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa

An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro sukashiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar.

Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun hada da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara hudu da haihuwa da kuma kaninta mai suna  Chibusoma.

Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu.

Majiyar labarinmu da rundunar ’yan sandan yankin Trans Ekulu sun amsa kiran gaggawar ne daga unguwar aka shaida musu faruwar lamarin inda su kuma ba su yi kasa a gwiwa ba suka rankaya zuwa gidan inda suka iske gawarwakin yara jina-jina.

Daga bisani dai ’yan sanda sun kwashe gawarwakin yaran zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Enugu, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Sule Ya Ƙara Musanta Zargin Kare Ƴan Ta’adda A Nasarawa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Gwamna Sule Ya Ƙara Musanta Zargin Kare Ƴan Ta’adda A Nasarawa
  • Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu
  •  Iran Ta Yi Kira Ga “FIFA” Da Ta Kori “Isra’ila” Daga Cikinta
  • Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC
  • PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
  • Kotu Ta Dage Shari’ar Zargin Cin Hanci Da Ake Yi Wa Shugaban KANSIEC Na Kano Zuwa Nuwamba
  • Libya Ta Tasa Keyar Baƙin Haure Yan Kasar Sudan 700 Zuwa Kasarsu
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin