Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
Published: 23rd, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga cikin sabbin sauye-sauyen akwai Sagir Muhammad Sani daga Ma’aikatar Ilimin Firamare zuwa Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da kuma Muhammad Yusha’u daga Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki zuwa Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi.
Sai Lawan Muhammad Haruna daga Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da kuma Injiniya Musa Alhassan Arobade daga Ma’aikatar Wuta da Makamashi zuwa Hukumar Bunƙasa Ma’aikata da Horaswa, wadda ke ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata na Jiha.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa, sabbin sakatarorin da aka nada su ne Garba D. Muhammad zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, da Kimiyya da Fasaha, da Fatima Aliyu Hadejia zuwa Hukumar Albashi da Fansho ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata.
Sauran sun haɗa da Baffa Abubakar wanda aka tura zuwa Ma’aikatar Ilimin Firamare, sai Bello Datti zuwa Sashen Kula da Harkokin Musamman/Al’amuran Majalisar Zartarwa ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, da Ibrahim Hassan zuwa Ma’aikatar Kuɗi, da kuma Nasiru Haruna zuwa Ma’aikatar Wuta da Makamashi, sai Umar Isah zuwa Hukumar Kula da Ma’aikata, yayin da Mahmud Isah Ringim aka tura shi zuwa Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu.
Shugaban Ma’aikatan ya ƙara da cewa, wannan sauyin zai fara aiki ne nan take.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Sakatarori zuwa Ma aikatar daga Ma aikatar zuwa Hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno
Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba.
Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin.
WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a BauchiBabban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce yawan ma’aikatan ne ya haifar da jinkiri wajen fara biyan mafi ƙarancin albashin.
Modu ya yi bayanin cewa a wasu lokutan gwamnatin tarayya na turo ƙasa da Naira miliyan 700 zuwa asusun ƙananan hukumomin domin biyan albashin, a wani yanayi da ake buƙatar Naira miliyan 778 domin biyan ma’aikata albashi.
Gwamnatin ta yi nuni da cewa, Jihar Kano da ke da ƙananan hukumomi 44 na da ma’aikata dubu 30,000 ne kawai, amma Borno da ke da 27 na da ma’aikatan ƙananan hukumomi da yawansu ya kai dubu 90,000.