Yahudawan Sahayoniyya Sun Bullo Da Dabarar Kisa Kan Falasdinawa Musamman ‘Yan Gudun Hijira
Published: 23rd, July 2025 GMT
Wani sabon salon gwamnatin mamayar Isra’ila na neman kashe Falasdinawa ‘yan gudun hijira da tsananta yunwa kansu
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun rufe tekun ga masunta da ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, matakin da ke kara dagula al’ummar Gaza da aka killace.
Gabashin tekun kudancin Gaza shi ne mashigar da mazauna yankin da kuma ‘yan gudun hijira a dukkanin yankunan zirin Gaza, musamman a kudancin zirin Gaza, biyo bayan umarnin ficewa da sojojin mamayarr Isra’ila suka bayar ga mazauna yankin Al-Mawasi da ke yammacin yankin.
Tekun ya zama mafaka daya tilo ga ‘yan gudun hijira da mazauna yankin saboda hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kan Falastinawa. Sai dai rundunar sojin mamayar Isra’ila ta sanya sabbin takunkumi kan Falasdinawa, musamman masunta, da masu ruwa da tsaki, da masu gudun hijira, tare da hana su shiga cikin teku kwata-kwata, ko don kamun kifi ko wata manufa ta daban.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka.
“Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen duniya da gaza aiwatar da dokokin kasa da kasa, yana mai cewa, “Shiru da kasashen duniya suka yi, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin kasashen duniya, musamman na kasashen musulmi da larabawa.
Da yake ishara da kiraye-kirayen baya-bayan nan da kasashe sama da ashirin suka yi na a dakatar da yakin, Sheikh Qassem ya yi ishara da cewa irin wadannan kalamai da cewa ba su isa ba ko kadan, Ya ce, “bai isa ba a ce kasashe 25 sun yi kira da a dakatar da yakin Gaza, wannan furucin kadai bai wadatar ba.
Sheikh Qassem ya yi kira da a kakaba takunkumi kan “Isra’ila”, da gurfanar da su a gaban shari’a, da kuma dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.