UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi
Published: 23rd, July 2025 GMT
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin kuɗi da ya danganci makomar yara.
Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Muhammad Farah, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida kan kasafin kuɗi mai la’akari da bukatun yara, inda ya gabatar da wasu alkalumma masu tayar da hankali dangane da rayuwar yara a jihar.
Farah ya ce jihar Kano na da yara fiye da miliyan 6 da rabi da ke ƙasa da shekaru 18, wadanda da dama daga cikinsu na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar mace-macen yara, ƙarancin abinci mai gina jiki, da kuma rashin samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.
Ya bayyana cewa, bisa ga rahoton MICS na 2021, yara 143,000 na mutuwa kafin su kai shekara biyar, yayin da kusan yara miliyan 2 da 900,000 ba su da cikakken rigakafi, sannan fiye da yara miliyan 4 na rayuwa cikin talauci.
Haka kuma, sama da yara miliyan 2 300,000 da suka kai shekarun makaranta suna zaune a gida ba tare da samun ilimi ba, wani hali da ya ce ya zama wajibi a sauya shi ta hanyar karfafa kasafin kuɗi na kula da yara.
Ya ce duk da wasu sauye-sauye da ake yi, fannin walwalar al’umma a Kano har yanzu na samun ƙarancin kudi, inda ya zargi sauyin kasafi da rashin daidaito a fannonin lafiya, ilimi da kare hakkin yara da janyo cikas ga cigaba.
Farah ya bayyana kasafin kuɗi mai kula da yara a matsayin wata dabara mai mahimmanci, fiye da ware kuɗi kawai ga makarantu da asibitoci.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Butu Butu, ya tabbatar da kudurin majalisar na tabbatar da cikakken aiwatar da kasafin kuɗi ga ma’aikatu da hukumomi.
Sai dai ya soki wasu shugabannin ma’aikatu da hukumomi da rashin kokarin karɓar kuɗaɗen da aka ware musu da kuma gazawar aiwatar da su, duk da kokarin bangaren zartarwa wajen sakin kudin. Ya bayyana cewa kimanin kashi 35% na kasafin kuɗin jihar na zuwa fannin lafiya ne da ilimi.
Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron, ciki har da ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da ma’aikatun gwamnati, sun yi kira ga gwamnatin Kano da ta tabbatar da kasafin kuɗi mai la’akari da yara, ta ƙara yawan kuɗaɗen da ake warewa shirye-shiryen kula da yara, tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana a wajen aiwatar da kasafin.
Daga Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a BornoDa yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.
“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.
A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.