Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati.

A jiya Laraba ne dai Muhammad Ridha Shaibani ya kai ziyara birnin Doha  inda ya gana da ministan na kasar ta Katar  Muhammad al-Khalifi domin yin shawara akan Syria.

Shaibani ya bayyana mahangar Iran akan Syria, da  ya kunshi ganin an shigar da kowane bangare na al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da kasar, ya kuma zama sun taka rawa wajen ayyana makomar kasar.

A nashi gefen ministan na kasar ta Katar Muhammad al-Khalifi ya yi ishara da rawar da Iran take takawa a cikin wannan yankin da kuma tasirisnta, haka nan kuma ya bayyana wajabcin ci gaba ta tuntubar juna  domin musayar ra’ayi akan halin da kasar ta Syria take ciki.

Haka nan kuma bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike

Rahotonni sun tabbatar da cewa: Da tsakar daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila dauke da motocin soji guda hudu da wasu sojoji masu tafiyar kafa sun kutsa cikin yankunan kasar Siriya daga titin Al-Hurriya, inda suka wuce titin Al-Kassarat, zuwa Talat Jabata Al-Khashab.

Majiyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta bayyana cewa: Sojojin mayar sun kafa shingen binciken ababen hawa inda suka tsaya suna binciken ababan hawa da ke wucewa, sannan suka haska wuta don gano hanyar kafin su fita ta hanyar da suka shiga. Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma suna shawagi a sararin samaniyar birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya.

A jiya Litinin ma, sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu sansanoni na rundunar sojin ta 36 ta musamman da aka fi sani da Ain al-Burj a gabashin kauyen Qala’at Jandal da ke cikin karkarar birnin Damascus, tare da kafa wani sansanin soji a saman dutsen Barbar domin sa ido kan motsin da ake yi a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya