Nijar : An nada Janar Tiani, a mukamin shugaban rikon kwarya
Published: 27th, March 2025 GMT
A Jamhuriyar Nijar, an daga martabar Abdourahmane Tiani madugun juyin mulkin sojin kasar daga mukamin Birgediya Janar zuwa Janar, mukamin soji mafi girma a kasar.
An ba Abdourahmane Tiani wannan mukamin ne bayan tabbatar masa da mukamin shugaban rikon kwarya na kasar a bikin da aka gudanar a jiya Laraba a Yamai babban birrin kasar.
Kafin hakan kuma Janar Abdourahamane Tiani, ya sa hannu kan dokar tsarin mulki na wucin gadi, mai taken “Tsarin farfado da Nijar”.
Bisa wannan doka, Tiani zai jagoranci kasar tsawon shekaru 5 tun daga ranar kaddamar da dokar, yayin da ainihin wa’adinta zai danganta da halin tsaro, da bukatun farfadowar kasar, da kuma ajandar kawancen kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.
Hukumomin wucin gadin sun kunshi shugaban jamhuriyar Nijar, da kwamiti mai kula da harkokin tsaron kasar, da gwamnati da kwamitin sulhu, da hukumar sa ido kan harkar jin kai da sauransu.
Wata dokar kuma da shugaban rikon kwaryar ya sanya wa hannu a jiya ita ce ta rusa dukkanin jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar.
An amince da wannan sabon tsarin mulki ne bisa kudurorin da aka tattara, a yayin taron farfado da kasa da aka gudanar a tsakanin ranakun 15 zuwa 19 ga watan da ya gabata a birnin Yamai, fadar mulkin kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran
A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya.
A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance kasa da abin da ake bukata, bisa la’akari da dama da karfin da bangarorin biyu ke da shi.
A yayin ganawar, Aref ya tunatar da ziyarar da ya kai birnin Qairawan na kasar Tunusiya shekaru ashirin da suka gabata, lokacin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar na farko na Jamhuriyar. Ya kara da cewa a lokacin yana jin kamar ya ratsa daya daga cikin garuruwan Khorasan na kasar Iran, yana daukar birnin Qairawan wata alama ce ta hadin kan al’ummar musulmi da alakar al’adu da addini tsakanin Iran da Tunisiya.