Sarkin Kano Na 15 Ya Soke Hawan Daba Saboda Matsalar Tsaro
Published: 27th, March 2025 GMT
Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bikin Sallar Eid-el-Fitr Durbar, saboda matsalar tsaro da ya sa aka dakatar da shirye-shiryen.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa ta karamar hukumar Nasarawa da ke Kano.
Ya kuma jaddada cewa zaman lafiya a tsakanin jama’a ya fi muhimmanci fiye da bikin Durbar.
Bayero ya yi nuni da cewa manyan Malaman addinin Musulunci da dattawa da masu ruwa da tsaki da ‘yan majalisarsa suka bada shawarar a soke bikin domin a samu zaman lafiya.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar Kano da su yi amfani da lokacin bukukuwan Sallah wajen ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki, tare da shaida yadda bikin Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ya yi addu’ar Allah ya jikanmu da rahama albarakcin wannan watan na Ramadan tare da fatan al’ummar Kano za su kasance cikin masu samun gafara da rahama.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sarki na 15
এছাড়াও পড়ুন:
Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu
Rundunar Ƴansandan jihar ba ta fitar da bayani kai tsaye ba, amma wani babban jami’i da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da kama wanda ake zargi, tare da ce wa an tafi da shi zuwa Lokoja domin cigaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp