Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
Published: 23rd, July 2025 GMT
“Mun kasance muna jiran a ba mu garin alkama, saboda muna jin yunwa sosai, muna neman abin sha da abinci, kwatsam tankokin sojan Isra’ila suka zo suka kewaye mu, suka fara harba bindiga a kanmu, ba mu iya motsawa ba. Ba mu samu gari ba, an kuma kewaye mu na tsawon sa’a daya da rabi zuwa biyu, wasu sun gudu, wasu an kashe su, wasu kuma sun ji raunuka.
Tsawon kwanaki 140 ke nan da Isra’ila ta rufe hanyoyin shiga Gaza. A halin yanzu, kashi 93% na iyalai a Gaza ba su da ruwan sha, kuma fiye da kashi 87% na yankunan Gaza sun zama yankunan soja ko kuma sassan da mazauna wurin suka bar muhallansu, kusan mutane miliyan 2.1 aka tilasta musu shiga wani karamin yanki, ba su da abubuwan da ake bukata na yau da kullum. Isra’ila ta hana shigar da kayayyakin agaji, da garin madarar jarirai da man fetur, wanda ya sa abinci da magunguna suka kusan kare a Gaza. Fararen hula na Gaza da dama da suka je wuraren rarraba kayayyakin agaji na Isra’ila da ake kira “Gaza Humanitarian Foundation” (GHF) sojojin Isra’ila ne suka harbe su. Firaministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya ce adadin wadanda aka kashe ya wuce 995. A Gaza, Isra’ila tana amfani da yunwa a matsayin makami, har ma wuraren rarraba abinci sun zama “tarkon mutuwa”, mutanen Gaza ba su samu gari ba, a maimakon haka ana kashe su da harbin bindiga.
A ranar 21, kakakin harkokin wajen kasar Sin ya jaddada cewa bai kamata a rika kai wa fararen hula hari ba, kuma bai kamata masu ba da agaji na kasa da kasa su fuskanci barazanar tsaro ba. Bugu da kari, kwanan nan kasashe 25 sun fitar da sanarwar hadin gwiwa suna bukatar a kawo karshen yakin yankin Gaza nan take, tare da bukatar Isra’ila ta bi dokokin kasa da kasa na jin kai, da kuma soke takunkumin da aka sanya na shigar da kayayyakin agaji.
Da fatan gwamnatin Isra’ila za ta saurari kiran kasa da kasa na kada ta yi amfani da “yunwa a matsayin makami”. Da kuma gaggauta dakatar da yakin nan take a yankin Gaza, don ba da damar shigar da kayayyakin agaji cikin sauki, tare da tabbatar da hakkin fararen hula.(Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kayayyakin agaji Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan.
Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka.
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — TrumpMinistan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin.
A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen tashin hankalin.
A ƙarshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na ƙarshe a yammacin Darfur.
Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyaɗe da fashi har ma da hare-hare kan ma’aikatan agaji.
Wata Kungiyar Likitoci ta MSF a ranar Asabar ta ce ana fargabar dubban fararen hula sun maƙale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher wanda ya koma hannun dakarun RSF.
Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, bayan taƙaddama ta siyasa tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin ƙasar, da Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), Kwamandan RSF.
Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan yadda za a haɗa rundunar RSF da sojojin ƙasar bayan juyin mulkin 2021 da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula.
Tun daga lokacin, yaƙin ya zama wani mummunan bala’i na jin kai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce fiye da mutane miliyan bakwai sun tsere daga gidajensu, yayin da dubbai ke buƙatar taimakon gaggawa.