Leadership News Hausa:
2025-09-18@00:36:49 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20]

Published: 28th, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20]

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]

Fashin Baƙi:

Maganar Ibn Juzai tana nuni ne ga girman tasirin salatin Annabi (S.A.W)i a rayuwar Musulumi, musamman dangane da ƙaunar Annabi Muhammad (S.A.W) da bin sunnarsa. Domin cikakken bayani kan wannan batu, bari na ɗan zurfafa bincike a cikin abubuwan da ke cikinsa.

Ma’anar Salati
A fagen ilimi, salati ga Annabi (S.A.W) na da fassarori da dama:

Idan Allah ne Yake yin Salati: Yana nufin yabo da ɗaukaka ga Annabi (S.A.W) da Allah Yake yi masa a wajen mala’iku. Idan Mala’iku ne Suka yi Salati: Yana nufin nema wa Annabi (S.A.W) rahama da ɗaukaka, da daraja da martaba a wurin Allah. Idan Musulumi Suka yi Salati: Yana nufin nema wa Annabi (S.A.W) albarka da gafara, da ɗaukakar daraja da girma da matsayi wurin Allah.

Allah Ya barta mana cewa:” Lalle Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku mummunai! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama mai yawa” Suratul Ahzãbi aya ta 56.

Wannan aya tana nuna cewa yin salati wajibi ne, kuma yana da babbar lada.

Salatin Annabi Yana Kawo Ƙaunar Annabi(S.A.W):

Domin a fahimci wannan batu, sai mu tambayi kanmu: Ta yaya mutum yake ƙaunar wani? Amsa a nan ita ce: Yana ƙaunar wanda yake yawan tunawa ne, kuma yana ƙaunar wanda yake amfana da shi ne a rayuwa, ya kuma ƙaunar wanda yake tare da shi a zuciya. Salati ga Annabi (S.A.W) yana ƙara ƙaunarsa domin Ya na yawan tunatar da Musulumi Annabi (S.A.W).

Yayin da mutum yake yawan yin salati, hakan yana sa zuciyarsa ta cika da tunanin Annabi (S.A.W), har ya zama yana ƙaunar sa fiye da kansa. Annabi (S.A.W) ya bayyana cewa: ”Ɗayanku ba zai zama cikakken mummuni ba har sai na zamnto Ni ne na fi soyuwa a gare sa sama ɗansa da mahaifinsa da mutane baki ɗaya.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Salati Yana Jawo Amsawar Annabi (S.A.W):
Annabi (S.A.W) ya ce: “ Babu wani da zai yi min salati face Allah Ya dawo min da ruhina har sai na amsa masa” Hadisi ne ingantacce Abū Dãwūd da Ahmad ne suka ruwaito.

Wannan yana nuna cewa salatin da Musulumi yake yi yana isa ga Annabi (S.A.W), kuma yana jin sa. Idan Musulumi yana da wannan fahimta, tabbas ƙaunarsa ga Annabi (S.A.W) za ta ƙaru.

Salati Yana Ƙara Fahimtar Rayuwar Annabi (S.A.W):
Duk wanda yake yawan yin salati, zai shiga neman ilimi game da halayen Annabi (S.A.W), da maganganunsa da ayyukansa. Wannan zai sa ƙaunarsa ta ƙaru, kamar yadda mutum ke ƙaunar wanda ya san halinsa.

Salati Hanya ce Ta Shiga Aljanna:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Duk wanda ya manta yi min salati, to ya kuskure hanyar shiga Aljanna “ Hadisi ne ingantacce Ibnu Maja ne ya ruwaito. Wannan yana nuna yin salati ga Manzon Allah (S.A.W) hanya ce ɗoɗar ta shiga Aljanna.

Salati Na Sanya Mutum Ruƙo da Sunna:
Bin sunna yana nuna ingantacciyar ƙaunar Annabi (S.A.W). Idan mutum ya san cewa yin salati yana ƙara masa kusanci da shi, zai so yin koyi da shi a aikace. Allah Ya ce:” Ka ce: In kun kasance kuna son Allah, to ku yi min biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai” Suratu Ãli Imrãn aya ta 31.

Salati Yana Ƙarfafa Son Bin Annabi (S.A.W):
Duk wanda yake yawan yin salati zai fi son yin koyi da Annabi (S.A.W) a cikin salla, da hulɗa da jama’a, da ibada da kuna mu’amala.
Idan mutum yana yawan yin salati, zuciyarsa tana son yin koyi da halayensa na gaskiya, kamar riƙon amana, da tausayi, da sanin ya kamata.

Salati Yana Hana Saɓa wa Annabi (S.A.W):
Duk wanda yake yawan yin salati, zai fi jin nauyin yin saɓo ko barin sunna. Domin yana sane da matsayin Annabi (S.A.W), kuma yana jin nauyin rashin bin hanyarsa.

Salati Yana Kawar da Tsauraran Ƙa’idojin bidi’a:
Yin salati yana hana mutum bin hanyoyin da ba sunna ba. Domin yana sane cewa abin da Annabi (S.A.W) ya bari, shi ne mafi alheri. Matuƙar mutum ya lazimci salatin da Annabi (S.A.W) ya zo da shi, to tabbas zai sami haka.

Fa’idoji Goma na Yin Salati ga Annabi (S.A.W)
-Yin salati yana da fa’idodi masu yawa, daga ciki akwai:
• Allah yana yin salati sau goma ga Musulumin da ya yi salati sau ɗaya.
• Ana gafarta wa mutum zunubi.
Ana ɗaga matsayi a Aljanna.
• Ana samun ceto (shafa’a) a ranar Alƙiyama.
• Ana samun waraka daga damuwa da baƙin ciki.
• Ana samun amsa addu’a.
• Ana kasancewa tare da Annabi (S.A.W) a ranar Alƙiyama.
• Ana samun kariya daga wahalar kabari.
Ana samun albarka a rayuwa.
• Ana samun kwanciyar hankali da soyayya a zuciya.

Hanyoyin yin salati suna da yawa, amma mafi inganci shi ne wanda Annabi (S.A.W) ya koyar, wato Salatin Ibrahimiyya
“Allahumma salli ‘ala Muhammadin wa ‘ala ali Muhammadin, kama sallaita ‘ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima, innaka hamidun majid. Allahumma barik ala Muhammadin wq ala Ali Muhammadin kama barakta ala Ibrahim wa ala Ali Ibrahim innaka hamidun majid.”

A taƙaice, wannan magana ta Ibn Juzai tana nuni ne ga cewa wanda yake yawan yin salati ga Annabi (S.A.W) zai ƙara ƙaunarsa kuma zai fi son bin sunnarsa. Idan muna son Annabi (S.A.W), dole ne mu yawaita yin salati gare shi. Idan muna son bin sunnarsa, dole ne mu yawaita tunawa da shi. Idan muna son rabauta a duniya da lahira, salati na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da za su kai mu ga hakan. Allah Ta’ala Ya sa mu kasance cikin masu yawan salati ga Annabi (S.A.W) da bin sunnarsa har mu kasance tare da shi a Aljanna!. Amin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan wanda yake yawan yin salati ƙaunar wanda ya Duk wanda ya bin sunnarsa salati yana Salati Yana

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.

Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala

A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.

“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).

“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.

Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki