An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara
Published: 28th, March 2025 GMT
Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama.
BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga.
Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana wasan ɓuya da jami’an tsaro da wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ’yan bindiga.
Ɗan jarida mai bincike kan harkokin ’yan bindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗan bindigar.
Isuhu Yellow ya yi fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne da rundunar California Army National Guard, mai dakaru sama da 18,000.
Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin AmurkaA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda Aminiya ta tabbatar, Isah ya mayar da martani kan jita-jitar cewa Amurka za ta ɗauki matakin yaƙi a kan Najeriya saboda zargin yi wa Kiristoci kisan gilla.
Ya bayyana cewa ba zai taɓa amfani da makami a kan mutanensa ba.
“Ba zan shiga Najeriya na kashe iyayena ba saboda ƙaryar cewa ana kashe Kiristoci,” in ji shi.
Ya ce duk da yake yana Allah-wadai da kashe-kashe da tashin hankali, bai kamata matsalar tsaro a Najeriya a danganta da wani addini ba.
“Ba zan ƙaryata batun kisan Kiristoci da Musulmai ba,” in ji shi.
“Shekau, Bello Turji, Dogo Gide da sauransu ba suna kai wa wani addini ɗaya hari ba ne kaɗai.”
Maganganun Isah na zuwa ne daidai lokacin Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi a kan Najeriya.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ba ta addini ba ce, inda ta ce matsalar na shafar Musulmai da Kiristoci baki ɗaya.