Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare
Published: 24th, July 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokokin Tarayya buƙatar ƙara ranto bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashin na gwamnatin tarayyar na 2025 zuwa 2026.
Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na yau Laraba.
Takartar ta ambato shugaban ƙasar na cewa karɓar rancen ya zama tilas saboda buƙatar ƙarin kuɗi da aka yi a aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, wanda ya tashi daga Dala miliyan 700 zuwa Dala miliyan 747 — ƙarin Dala miliyan 47 ke nan.
Idan ba a manta ba, a jiya Talata ne Majalisar Datttawan Nijeriya ta sahale wa shugaba Tinubu karɓo bashin Dala biliyan 21 daga ƙetare domin cike giɓin kasafin kuɗin kasar na bana zuwa baɗi.
Ko a watan Nuwambar 2023, majalisar wakilai da ta dattawa sun amince da ciyo bashin Dala biliyan 7 da miliyan 800, da kuma Euro miliyan 100 domin gudanar da manyan ayyuka da sauran ayyukan raya ƙasa.
Kazalika, a watan Maris ɗin 2025 ma majalisar ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan 21 da miliyan 500 daga ƙetare, da kuma karɓar takardun kuɗin banki da suka kai Naira biliyan 757 da miliyan 900 domin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu.
Ya zuwa watan Maris dai, adadin bashin da ake bin Najeriya ya kai Dala biliyan 91 kwatankwacin Naira tiriliyan 121, a cewar wani rahoton ofishin kula da basuka na ƙasar DMO.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai rance Dala miliyan daga ƙetare Dala biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga cikin sabbin sauye-sauyen akwai Sagir Muhammad Sani daga Ma’aikatar Ilimin Firamare zuwa Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da kuma Muhammad Yusha’u daga Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki zuwa Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi.
Sai Lawan Muhammad Haruna daga Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da kuma Injiniya Musa Alhassan Arobade daga Ma’aikatar Wuta da Makamashi zuwa Hukumar Bunƙasa Ma’aikata da Horaswa, wadda ke ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata na Jiha.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa, sabbin sakatarorin da aka nada su ne Garba D. Muhammad zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, da Kimiyya da Fasaha, da Fatima Aliyu Hadejia zuwa Hukumar Albashi da Fansho ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata.
Sauran sun haɗa da Baffa Abubakar wanda aka tura zuwa Ma’aikatar Ilimin Firamare, sai Bello Datti zuwa Sashen Kula da Harkokin Musamman/Al’amuran Majalisar Zartarwa ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, da Ibrahim Hassan zuwa Ma’aikatar Kuɗi, da kuma Nasiru Haruna zuwa Ma’aikatar Wuta da Makamashi, sai Umar Isah zuwa Hukumar Kula da Ma’aikata, yayin da Mahmud Isah Ringim aka tura shi zuwa Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu.
Shugaban Ma’aikatan ya ƙara da cewa, wannan sauyin zai fara aiki ne nan take.
Usman Muhammad Zaria