Karin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arzikin Duniya
Published: 28th, March 2025 GMT
Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji.
La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani sabani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana
Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP.
Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni mai nazari ne, kuma ina nazarin ra’ayoyi, a jihohin Arewa Peter Obi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP zai doke duk wani ɗan takara, saboda mutanenmu suna da gaskiya.”
Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar KwastamPeter Obi ya fice daga Jam’iyyar PDP a watan Mayun 2022 inda ya jagoranci Jam’iyyar LP a zaɓen 2023.
Da yake waiwayen tushen PDP, jigon na PDP ya tunatar da ’yan Najeriya irin ƙarfin da jam’iyyar ke da shi da kuma rawar da take takawa wajen maido da mulkin dimokraɗiyya.
Ya ce, “Dole ne in shaida cewa mutane da yawa sun manta cewa an kafa Jam’iyyar PDP ne a matsayin ƙungiya mai zaman kanta, a shekarar 1998 aka kafa mu, sannan muka shiga zaɓe a 1999, muna cikin kowace rumfar zaɓe, domin mu ne muka ci zaɓen farko.
“Mutane da yawa sun manta cewa PDP ce ta lashe mafi yawan ƙananan hukumomi, lokacin da aka zo batun zaɓen shugaban ƙasa, mun ci zaɓen shugaban ƙasa, mun ci na majalisar dattawa, muka ci majalisar tarayya, mu ne ke riƙe da madafun iko, shi ya sa muka yi matuƙar farin ciki da cewa mun maido da dimokuraɗiyya a Najeriya, muka sake kafa mulkin farar hula.
“Saboda shekaru da dama ana mulkin soja, amma mun samu nasarar kawo ƙarshen hakan ta hanyar dimokuraɗiyya, don haka PDP ta kasance jam’iyyar talakawa ce, shi ya sa idan muka ce mulki ga jama’a, muna nufin hakan ne saboda abin ya kasance, kuma ya kasance haka.”