Aminiya:
2025-07-24@04:08:27 GMT

Ambaliyar Mokwa: Yawan mutanen da suka salwanta ya haura 700

Published: 3rd, June 2025 GMT

Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata.

Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da ta gabata da daddare.

Ɗaruruwan gidaje sun lalace, inda mutane da yawa suka rasa matsugunansu.

Kafar yaɗa Labarai ta BBC ta ruwaito a ranar Litinin cewa yawan mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa sama da 200, kuma an dakatar da ayyukan ceto saboda hukumomi sun yanke ƙauna daga samun wasu da rai.

Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabo Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindiga

Mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda ambaliyar ta rutsa da su, ciki har da almajirai masu yawan gaske a makarantun tsangaya a yankin.

Musa Kimboku, wani jami’in yankin, ya tabbatar da dakatar da ayyukan ceto. Hakimin Mokwa, Muhammadu Aliyu, ya bayyana cewa ba a iya haƙo wasu gawarwaki ba saboda sun shiga “ta Kogin Neja.”

Basaraken ya ƙara da cewa za a fara tono gawarwakin da suka maƙale a karkashin ƙasa domin hana yaduwar cututtuka.

Wani magidanci da ya rasa matarsa da jaririnsu a ambaliyar, Malam Adamu Yusuf, ya ba da labari: “Ina kallo amma babu abin sa zan iya na taimako yayin da ruwa ya share iyalina. Na tsira saboda ina iya yin iyo.”

Saliu Sulaiman, wani mazaunin yankin, yace ya rasa kusan $1,500 – kudin da ya samu daga sayar da kayan gonarsa – kuma ya rasa matsuguninsa.

Mazauna yankin suna zargin cewa fashewar wani madatsar ruwa da ke kusa ta ba da gudummawa ga tsananin ambaliyar ruwa, wanda har yanzu hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.

Karfin ruwan ambaliyar ya kasance mai tsanani har ma an ga gawarwaki a garin Rabba, wanda ke da nisan tafiyar awa daya daga Mokwa.

Musa Kimboku na Karamar Hukumar Mokwa ya umurci kauyukan da ke makwabta da su binne “duk wata gawa da suka samu.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) ya ruwaito wani masunci na yankin Danjuma Shaba, wanda ya rasa gidansa na cewa, “Ba ni da wurin kwana. Gidana ya riga ya rushe.”

Farida Auwalu, wacce ita kadai ce ta tsira da cikin ’yan uwanta 16, ta rasa ’ya’yanta bakwai a ambaliyar. An gano gawarwakin huɗu daga cikin yara an binne su.

“Fatana shi ne in ga sauran gawarwaki kuma in yi musu jana’izar da ta dace don samun nutsuwa,” in ji ta.

Waɗanda suka tsira daga ambaliyar ruwa suna ƙoƙarin samun taimakon farko.

Hassan Umar, wani mazaunin yankin, ya shaida wa Al Jazeera cewa waɗanda abin ya shafa ba su da kuɗi ko abinci, inda akasarinsu ke kwana a fili.

Ambaliyar ta haddasa rugujewar gadar da ta haɗa yankunan Koshaba da Rabba, kimanin kilomita 7 daga garin Mokwa, inda ruwan ambaliyar ya hadu da Kogin Neja, inda aka gano gawarwaki da yawa a wurin da ruwan ya hadu da kogin.

Alhaji Tanko Bala, shugaban al’ummar Hausawa a Mokwa, ya bayyana a karshen mako cewa mafi yawan waɗanda abin ya shafa suna kwana a fili saboda babu ingantattun tanadi daga gwamnati don samar musu da matsuguni.

Ya soki sansanin da aka keɓe a makarantar firamare a matsayin wanda ba za a iya zama a ciki ba kuma ba shi da kayan bukatun yau da kullum, yana mai kira ga gwamnati da ta taimaka wa wadanda abin ya shafa da kayan kwanciya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliya Mokwa a ambaliyar

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi

Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila

Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan ‘yan gwagwarmaya da kuma fitattun al’umma da masanan Falasdinawa, biyan ladar moro-maron yahudawan sahayoniyya ne da jami’an hukumar Falasdinu suka ci.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ruguza gidajen mutane a Jenin, tare da koran dubban mutane a Tulkarm, ana kuma kwace yankunan mutane a gabar yammacin kogin Jordan.

Shadid ya bayyana cewa: Wadannan ayyuka suna nuna manufar Hukumar Cin gashin Falasdinawa ne na ganin ta raba ‘yan gwagwarmaya da yankin gabas yammacin kogin Jordan, tare da barin Falasdinu a bude ga sojojin mamayar Isra’ila gungun ‘yan ta’addan su aiwatar da tsare-tsaren Sanya Falasdinawa gudun hijira.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe
  • Eritrea ta gargadi Habasha game da yunkurin kafa tashar jiragen ruwa a cikin yankinta
  • WHO Ta Buƙaci Isra’ila Ta Saki Ma’aikacinta Da Aka Kama A Gaza
  • Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
  • Magudnar Ruwa Ta Yi Ajalin Rayuka Hudu A Zangon Kaya, Kano
  • Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni
  • Jaridar Washington Post Ta Ce; Yeman Ta Gurguta Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Isra’ila
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi