Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindiga
Published: 3rd, June 2025 GMT
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa.
A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja.
A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne.
Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan.
A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci Naira miliyan 10, amma bayan iyalansa sun yi karo-karo sun biya, sai ’yan ta’addan suka nemi ƙarin Naira miliyan 20 da sababbin babura ƙirar Bajaj, sa’nnna suka yi barazanar kashe ma’auratan idan ba a ba su ba.
A farkon watan Mayu 2025, suka bindige amaryar tasa mai suna Lami, a ƙoƙarinsu na matsa wa iyalan su biya musu buƙata.
Uwar gidarsa mai suna Maimuna, ta tabbatar wa Aminiya cewa an sake shi a wani daji da ke kusa da yankin Kotonkoro a Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja, bayan da iyalan suka biya ƙarin Naira miliyan 20.
Malama Maimuna ta bayyana farin cikinsu, amma ta ce Malam Yakubu bai riga ya ya iso gida ba a lokacin.
Ta bayyana cewa a watan Nuwambar 2024 sai da suka sayar da kusan duk abin da suka mallaka domin haɗa Naira miliyan 10 da aka buƙata, wanda ƙanin mijin nasu ya kai wa ’yan bindigar a wani daji a Jihar Kebbi.
Ta ce bayan nan ne ’yan ta’ddan suka nemi ƙarin Naira miliyan 60 amma daga ƙarshe aka daidaita da su a kan Naira miliyan 20 da sababbin babura guda huɗu, buƙatar a iyalan suka yi ƙoƙarin biya kafin a sako shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Garkuwa Kontagora ƙarin Naira miliyan Naira miliyan 20
এছাড়াও পড়ুন:
NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar.
A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a cikin shekarar nan, lamarin da ke nuna yadda safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa a ƙasar.
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a NijarCikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jami’anta sun kama mutanen ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, bayan sun samu bayanan sirri da suka taimaka wajen gano su.
NDLEA ta bayyana cewa ƙwayoyin Tramadol ɗin da aka gano an shigo da su ne cikin kwalaye a matsayin maganin multivitamins, yayin da ake ƙoƙarin fitar da su daga filin jirgin a wasu manyan motoci.
“Ƙwayoyin da aka kama ba su da wata alaƙa da amfani na lafiya, waɗanda aka shigo da su a ɓoye a matsayin maganin rage kasala da ƙara kuzari (multivitamins),” in ji sanarwar NDLEA.
Rahotanni sun nuna cewa a da likitoci na bayar da Tramadol ne don rage zafi da raɗaɗin ciwo, amma yanzu ta zamo annoba musamman a tsakanin matasa, wadda ke haddasa mummunan maye da illa ga lafiya.
Hukumar ta nuna damuwa game da yadda yawan masu amfani da Tramadol ke ƙaruwa ba wai a Najeriya kaɗai ba, har ma a wasu ƙasashen Afirka, duk da illolin da ƙwayar ke haddasawa, kamar matsalolin taɓin hankali ko ma rasa rai gaba ɗaya.