Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Wani Kisan Kiyashi Kan Masu Bukatar Kayan Agaji
Published: 3rd, June 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji
Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza.
Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma har yanzu ba a san ko su waye ba.
Wannan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, wanda ke nuni da irin mummunan halin jin kai da fararen hula ke fuskanta a zirin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”
Ofishin Fira ministan kasar Iraki ya fitar da bayani a yau Laraba akan abinda ya gudana a tsakanin Muhammad Shiya al-Sudani da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a tattaunawar wayar tarho.
Sakataren harkokin wajen Marco Rubio ne ya kira yi fira ministan Iraki inda su ka tattauna alakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki a wannan yankin.
Sudani ya yi ishara da hare-haren bayan nan da aka kai wa cibiyoyin man fetur dake yankin Kurdistan na Iraki da kuma yankin Salahuddin a Karkuk.
Haka nan kuma ya ce a halin yanzu jami’an tsaro suna gudanar da bincike domin gano wadanda su ka kai harin.”
Haka nan kuma Fira ministan na kasar Iraki ya bayyana mamakinsa akan yadda kai harin ya faru a lokacin da aka kulla yarjejeniya a tsakanin ma’aikatar man fetur din Iraki da kuma kamfanoni masu zuba hannun jari daga Amurka.”
Fira ministan harkokin wajen na Iraki ya kuma yi Magana akan rundunar sa kai ta “Hashdus-sha’abi” yana mai cewa; ana yi wa dokokin tsaron Iraki kwaskwarima ne a gaban majalisar da zai shafi rundunar sa-kai din wacce cibiya ce da Iraki ta amince da ita a gwamnatance.