NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa
Published: 3rd, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ambaliyar ruwa na ci gaba da raba dubban mutane da matsugunansu, tare da lalata dukiyoyi a faɗin Najeriya.
Ko a makon da ya gabata, wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun fuskanci irin wannan ambaliya da ta yi sanadiyyar rasa ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Ko waɗanne hanyoyi za a bi domin kauce wa ɓarnar ambaliya a Najeriya?
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa kaucewa ambaliyar ruwa Mokwa
এছাড়াও পড়ুন:
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.