Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin gwauron zabo
Published: 3rd, June 2025 GMT
Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki.
Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa.
Wannan hauhawan farashin, wana ta zarce abin da aka saba gani a lokutan rani, ya kasaara ƙarfin iyalai yin sayayya domin girki abincin Sallah, wanda hakan ya haifar da damuwa, musamman a jihohin Kano, Taraba, Kwara, da Jigawa.
Al’umma a Jihar Kano sun koka bisa mummunan tasirin wannan tsadar rayuwa. Wani ma’aikacin gwamnati mai ’ya’ya biyar, Malam Idris Bako, ya nuna damuwarsa.
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindigaMalam Idris ya bayyana cewa, a baya a irin wannan lokaci an saba ganin kayan lambu sun yi arha, magidanta sun fi mayar ba da fifiko ga batun dabbar layya.
Ya ce amma a bana lamarin ya juya, “ma’ikata ba sa lissafin sayen abin layya saboda tsadar dabbobi. Abin takaici, mun yanke shawarar yin abinci mai kyau da sallah kuma mu jira baɗi, amma halin da ake ciki a yanzu ya kawo mana babbar damuwa.
“Kayan lambun da muke shirin saya don miyan Sallah suna neman fin da ƙarfinmu. Ƙwandon tumatir da ake sayarwa N12,000 a makon jiya, yanzu ya kai N35,000,” in ji shi.
Wata mata da ke zaune a unguwar Ja’oji, Malama Halima Bello, ta bayyana halin da ake ciki a matsayin mafi tsanani sa ta taɓa gani a shekaru talatin da suka gabata.
Ta nuna cewa iyalai da yawa sun watsar da shirinsu na yin layya saboda tsadar dabbobi, ga shi kuma yin miya mai kyau da Sallah ma na neman ta gagara.
Malama Hakima ta ce “Kwandon attarugu yanzu N40,000 yake, saɓanin N25,000 da aka sayar a wancan makon. Yana da matuƙar wahala ga iyalai yanzu su yi girkin Sallah yadda suka tsara d farko.”
A ziyarar da muka kai kasuwar kayan lambu ta ’Yan Kaba, mun lura cewa akwai matsakaicin wadatar kayan gwari, amma kuma babu masu zuwa saye sosai.
Farashin kwandon tumatir, wanda aka sayar da shi N11,000 zuwa N13,000 a makon da ya gabata, yanzu ya koma tsakanin N28,000 zuwa N35,000. Haka kuma, ana sayar da kwandon barkono kusan N43,000.
Mansur Simon, wani mai sayar da tumatir a Kasuwar ’Yankaba, ya danganta hauhawar farashin kayan da ƙaruwar buƙatun jama’a a lokacin sallah, yana mai cewa an saba ganin hakan.
Farashi ya ninku sau 3 a mako 2Haka lamarin yake a kasuwannin Jihar Taraba, inda farashin kayan lambu ya yi irin wannan tashin gwauron zabo.
A babbar kasuwar kayan lambu ta Jalingo farashin barkono, albasa, barkono, tumatir, karas, da kabeji sun ninka har sau uku a cikin makonni biyu.
Babban kwandon sabon tumatir, wanda aka sayar N8,000 watanni biyu da suka gabata, ya koma N35,000 zuwa N40,000. Buhun barkono mai nauyin kilo 100, wanda a da N35,000 ne, yanzu ya koma N110,000.
Attarugu ya haura daga N40,000 zuwa N130,000, yayin da barkono mai yaji na Habasha, wani nau’i na musamman na yankin, ya haura daga N50,000 zuwa N160,000-N170,000.
Hatta busasshen barkono da albasa su ma sun yi irin wannan tashin gwauron zabo.
Muhammed Tukur, wani dillalin kayan lambu, ya bayyana cewa kayan sun ƙare a wuraren da ake kawo su daga jihohin Gombe, Bauchi, Zariya, da Yobe, kuma a halin yanzu ba a yi girbin na damina ba.
Ƙorafi a Kasuwar ShuwarinA Jihar Jigawa, a Kasuwar Shuwarin, Malam Isah Aƙilu, mai sayar da tumatir da barkono, ya bayyana yadda farashin ya ninka.
Buhun attarugu ya koma yanzu N125,000 zuwa N150,000, kwandon tumatir yana tsakanin N30,000 zuwa N40,000, buhun albasa kuma N25,000.
Malam Aƙilu ya bayyana cewa suna yawan samun ƙorafi daga abokan ciniki game da tashin gwauron zabon kayan lambu a kasuwar.
Ƙarin kashi 10 a KwaraJihar Kwara ma an samu tsadar tumatir. Bincike a kasuwanni a Ilorin ya nuna ƙaruwar farashin tumatir kashi 10 cikin 100, idan aka kwatanta da farashin makonni biyu baya.
Yanzu kwandon tumatir ya kai tsakanin N18,000 zuwa N70,000, ya danganci girma da ingancin kayan.
Wata ’yar kasuwa a Ilorin, Iya Aisha Alata, ta tabbatar da cewa kwandon da aka sayar N40,000 a makon jiya yanzu N50,000 ne.
Wata matar aure, Madam Nice Oladuni ta nuna damuwarta ganin yadda farashin ƙaramin kwandon da ta saya N2,500 a makon da ya wuce ya ninka zuwa N5,000 a ranar Lahadi.
Dalilin tsadar kayan miyaDuk da yake wasu suna danganta hauhawar farashin da bukukuwan Babbar Sallah, wasu kuma na ganin ambaliyar ruwa da aka yi kwanan nan a Jihar Neja, wadda ta kawo cikas ga sufuri ga jigilar kayayyaki, shi ne sababi.
Iya Aisha ta bayyana kyakkyawan fata cewa farashin na iya daidaita bayan Sallah, tana mai danganta hauhawar farashin da yanayi da bukukuwan Sallah.
Har ila yau, ta lura da sauye-sauyen hanyoyin samar da kayayyaki daga tumatirin Hausawa zuwa waɗanda ke fitowa daga Kudu maso Yamma, wanda ke ba da gudummawa ga bambancin farashi.
Ra’ayoyin ƙwararru kan tsadar kayan lambuAlhaji Sani Yadakwari, Shugaban Ƙungiyar Manoma, Masu Sarrafawa da Masu Kasuwancin Tumatir ta Ƙasa (NATPAN) reshen Jihar Kano, ya bayyana cewa ƙarancin kayan na yanzu na yanayi ne, saboda lokacin girbin kayan lambu ya riga ya wuce a yawancin wuraren da ake nomawa.
Ya ce wannan abu ne da ke faruwa a kowace shekara saboda rashin ingantattun hanyoyin adana kayan gwari, kuma ana sa ran farashin zai ragu idan aka fara girbin damina.
A halin yanzu, ɗauƙacin yankin Arewa na dogara ne wajen samun tumatir daga wasu yankuna a Jihar Kaduna, Jihar Katsina, Jihar Kuri’a Riba, da kuma wasu sassan Jihar Benue.
Lawan Adam, masanin tattalin arzikin noma mazaunin Kano, ya jaddada cewa mafita guda ɗaya tilo mai ɗorewa ita ce rungumar ingantattun hanyoyin adana kayan lambu.
Ya nuna cewa manoma na fama da asarar kayan gwari bayan girbi, wanda ke ba da gudummawa ga ƙarancin kayayyaki da tsadarsu a lokutan da ba na noma ba.
Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da yin asara na iya sa manoma su bar sana’ar noman kayan lambu.
Hanyoyin adanawa da manoma ke amfani da su a halin yanzu, musamman bushewa da rana, sun riga sun zama tsofaffi kuma marasa tsafta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Attarugu Bukukuwan Sallah kasuwa kayan gwari Kayan miya tashin gwauron zabo tashin gwauron zabo ya bayyana cewa farashin kayan da aka sayar da farashin kayan lambu kayan gwari
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga cikin sabbin sauye-sauyen akwai Sagir Muhammad Sani daga Ma’aikatar Ilimin Firamare zuwa Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da kuma Muhammad Yusha’u daga Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki zuwa Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi.
Sai Lawan Muhammad Haruna daga Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da kuma Injiniya Musa Alhassan Arobade daga Ma’aikatar Wuta da Makamashi zuwa Hukumar Bunƙasa Ma’aikata da Horaswa, wadda ke ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata na Jiha.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa, sabbin sakatarorin da aka nada su ne Garba D. Muhammad zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, da Kimiyya da Fasaha, da Fatima Aliyu Hadejia zuwa Hukumar Albashi da Fansho ƙarƙashin ofishin Shugaban Ma’aikata.
Sauran sun haɗa da Baffa Abubakar wanda aka tura zuwa Ma’aikatar Ilimin Firamare, sai Bello Datti zuwa Sashen Kula da Harkokin Musamman/Al’amuran Majalisar Zartarwa ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, da Ibrahim Hassan zuwa Ma’aikatar Kuɗi, da kuma Nasiru Haruna zuwa Ma’aikatar Wuta da Makamashi, sai Umar Isah zuwa Hukumar Kula da Ma’aikata, yayin da Mahmud Isah Ringim aka tura shi zuwa Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu.
Shugaban Ma’aikatan ya ƙara da cewa, wannan sauyin zai fara aiki ne nan take.
Usman Muhammad Zaria