Jiragen Yakin NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 20, ‘Yan Banga 2 A Zamfara
Published: 3rd, June 2025 GMT
Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi.
Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa.
“Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe ‘yan ta’adda sama da 20.
“Abin takaici, a yayin harin ta sama, ‘yan banga biyu a yankin, an kuskure su yayin da wasu kuma suka samu raunuka,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa.
Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Laraba, ya ce yayin da ake fama da yanayi mai sarkakiya, da sauye-sauye masu maimaituwa daga ketare, cinikayyar waje ta Sin na gudana lami lafiya, cike da karfin juriya da babban karsashi.
Hakan a cewarsa, ya shaida gazawar yakin haraji da cinikayya wajen girgiza fifikon da Sin ke da shi, a fannin raya masana’antun sarrafa hajoji da kasar ta gina a tsawon lokaci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp