Mutuwar kasko: Mai gida da dan fashi sun kashe juna a Abuja
Published: 2nd, June 2025 GMT
Wani magidanci ya yi mutuwar kasko da wani mai sana’ar jari-bola, bayan da gungun wasu ’yan jari-bola suka yi kokarin cire tagar gidansa da karfin tsiya a yankin Babban Birnin Tarayya.
Magidancin, wanda ke sana’ar sayar da tufafin gwanjo ya gamu da ajalinsa ne bayan bata-garin sun caka masa wuka a yankin Tsohuwar Kutunku da ke Karamar Hukumar Gwagwalada.
Wani dan unguwar mai suna Francis Nnamdi, ya ce da misalin karfe 9.26 na dare ne wasu mutum uku masu sana’ar bola-jari suka je gidan mutumin, suna kokarin cire karfen tagarsa.
Ya ce cewa bayan mai gidan ya gan su ne ya tunkare su domin jin dalilinsu na neman cire masa tagogi, inda a garin haka daya daga cikinsu ya zaro wuka.
Ganin haka ne mutumin ya shiga daki ya dauko adda, kuma a garin rikicin masu bola-jarin suka caka masa wuka, shi kuma ya mayar da martani ta hanyar saran dayansu da addar hannunsa, ragowar kuma suka tsere, suka bar dayan kwance a cikin jini.
Ma’aikatan Kotu Koli sun janye yajin aikin da suka shirya tafiya Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri neYa ce daga bisani makwabta suka kira ’yan sanda, suka dauke gawarwakin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda likitoci suka sanar cewa dukkansu sun mutu, aka ajiye gawarwakin a mutuware.
Mun nemi karin bayani daga kakakin ’yan sanda na Babban Birnin Tarayya, SP Adeh Josephine, amma ta shaida wa wakilinmu cewa ba ta samu rahoton lamarin ba, amma za ta bincika.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bola Jari Gwagwalada karfe
এছাড়াও পড়ুন:
Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta sanar da cewa a ’yan kwanakin nan za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu jihohi da ke sassa daban-daban na ƙasar.
Hakan na kunshe cikin hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025 da hukumar ta fitar.
Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a An nada ’yar Najeriya a Kwamitin Nukiliya na Majalisar Dinkin DuniyaNiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.
A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama.
Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, an samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sakkwato da Kaduna.
Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar kasar kamar Abuja da Neja da Filato da Nasarawa da Benuwe da Kogi su ma za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.
Ranar Talata da safe kuma ana sa ran ruwan sama da tsakar rana a Abuja da Kwara da Neja da Filato.
A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sakkwato da Taraba sannan daga baya za a samu a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.