Hajji ta bayan fage: Saudiyya ta hana mahajjata 269,000 shiga Makka
Published: 2nd, June 2025 GMT
Jami’an Tsaron Saudiyya sun kori mutane sama da 205,000 da ke neman yin aikin Hajji ta barauniyar hanya daga birnin Makka a yayin da aikin Hajjin bana ya kawo jiki.
Daraktan Tsaron Jama’a kuma Shugaban Kwamitin Tsaron Hajji, Laftanar-Janar Mohammed Al-Bassami, ya bayyana cewa hukumomin kasar sun hana mutane sama da 269,000 marasa takardun izini shiga Makka, da kuma motoci 110,000 dauke da mahajjata ba bisa ka’ida ba da aka hana shiga.
An kuma kama 1,239 da suka yi yunkurin jigilar mahajjata ba bisa ka’ida ba, tare da ci tarar masu karya dokokin Hajji sama da 75,000, kuma tare da bankado ofisoshin aikin Hajji na bogi sama da 415.
Laftanar Janar Mohammed Al-Bassami ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, a yayin da yake jawabi game da yadda suka tsaurara matakan taro domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin bana cikin tsari da bin doka.
Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwana 10 Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri neJami’in ya jaddada amfani da fasahar zamani don inganta tsare-tsaren tsaro, yana mai da nanata cewa jami’an tsaro suna sanya ido sosai kan duk wani mai karya doka, a kokarinsu na ganin an yin aikin hajjin bana cikin nasara.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata.
Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace.
Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa zai taimakawa dalibai su tashi da sun koyi abubuwan da zasu yi baya rayuwar da suka yi cikin aji.
A nashi jawabin mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa. Egbewole ya nuna farin cikinsa da godew a Shugaban kasa Tinubu kan yadda ya amince da gaiyar da Jami’ar ta yi ma shi, da kuma taimaka mata wajen tafiyar da bunkasar abubuwan jin dadi.
“Muna nan muna sa ido saboda ci gaban samun abubwan da suke taimakawa ci gaba kwarai da gaske a kowace rana kamar yadda yace yana da amincewa da yardarm ci gaba da samun hakan’’.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA