Fira Ministan Kasar Senegal Yana Ziyarar Aiki A Kasashen Yammacin Afirka
Published: 2nd, June 2025 GMT
A ranar Alhamis da ta gabata ce Fira ministan kasar Senegal Usman Sonko ya bude ziyarar aiki a kasashen yamamcin Afirka domin kara dankon zumunci da kasashen.
Daga cikin kasashen da ziyarar ta shafa dai akwai Cote-De Voire, Serra Lione, da Guinea Conakry .
A makon da ya gabata ne dai a yayin taron kira ga masu zuba hannun jari a kasar, senegak aka sanar da shirin ziyarar ta Fira ministan zuwa wadannan kasashe.
A Zangon farko na ziyarar a kasar Cote De Voire, fira ministan ya gana da Amadu Hot, wanda ya kasance dan takarar da Senegal ta tsayar, domin neman shugabancin Bankin Raya kasashen Afirka. Haka nan kuma ya gana da sabon shugaban Bankin na Raya kasashen Afirka, dan asalin kasar Mouritania Sidi Would Taha, ya kuma tattauna hanyoyin bunkasa dangantaka da bankin.
A kasar Guinea Conakri kuwa, fira minstan na Senegal ya gana da takwaransa Amadu Bah, inda suka tattauna hanyoyin bunkasa dangantaka a tsakanin kasashensu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro.
Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mu8hammad Bin Salman.
Bugu da kari Dr. Ali Larijani ya ce a yayin ganawarwa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman, sun tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashensu ta fuskoki mabanbanta, da kara girman wannan alakar ta fuskar tattalin arzki da tsaro fiye da yadda take a yanzu.”
Haka nan kuma ya ce, za a yi aiki domin kawar da dukkanin abubuwan da suke kawo cikas a kan hanyar bunkasa wannan alakokin.
Dr. Ali Larijani ya kuma ce,an yi shawara akan yadda kasashen yankin za su bunkasa alakarsu ta tsaro domin ganin an tabbatar da zaman lafiya.
Da aka tambaye shi akan ko an sami sauyi akan mahangar kasashen Larabawa bayan harin da HKI ta kai wa Qatar, Dr.Ali Larijani ya ce; Tabbas da akwai sauyi a cikin yadda kasashen larabawa suke Kallon abubuwan da suke faruwa, domin suna ganin cewa kasantuwar HKI a cikin wannan yankin yana hana zaman lafiya.
Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ziyarci Saudiyya inda ya gana da ministan tsaronta da kuma Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci