Saudiyya : Matakin Isra’ila na hana mu ziyaratar falasdinwa, watsi ne da tayin zaman lafiya
Published: 2nd, June 2025 GMT
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa
Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa.
A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya.
A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa da shugaban hukumar Falasdinu Mahmoud Abbas, a cewar Hussein al-Sheikh, mataimakin shugaban hukumar ta PA.
Wannan dai za ta kasance ziyara mafi girma da Saudiyya za ta kai yankin tun bayan da Isra’ila ta mamaya yankin a shekarar 1967.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ke kokarin ganin kasashen duniya su amince da Falasdinu a matsayin kasa.
Daga bisani Shugaban kungiyar kasashen Larabawa da ministoci hudu sun gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ta kafar Intanet.
Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Ba Zata Bar Tace Sinadarin Uranium Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta iya watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba
Ministan harkokin wajen na Iran ya fada a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Fox News cewa: Har yanzu ba a dakatar da inganta sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da aka mata bayan hare-haren da Amurka ta yi mata mai tsanani.
A cikin wata hira da gidan talabijin na Fox News, Araqchi ya ce, “Shin shirin inganta sinadarin Uranium a Iran ya dawo? Shin har yanzu wannan shirin yana ci gaba, ko kuwa barnar da aka yi ta yi tsanani har ta kai ga dakatar da shi gaba daya?” Ya ce: “Ba a dakatar da shi ba, duk da cewa barnar ta yi muni da yawa, amma ba shakka ba za a iya yin watsi da Shirin inganta sinadarin Uranium ba, domin wannan nasara ce ta masana kimiyyar Iran, kuma a halin yanzu abin alfahari ne ga kasar, kuma inganta sinadarin Uranium yana da matukar muhimmanci a gare ta.”
Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: “Iran ba zata taba matsawa wajen inganta sinadarin uranium da kashi 90 cikin dari ba. Iran ta himmatu wajen tabbatar da samar da makamashin Uranium kasa da kashi 5% domin samar da makamashin nukiliya. Kuma tana inganta sinadarin na Uranium zuwa kashi 20% saboda tana da injin binciken TRR.”