Ministan Harkokin Wajen Iran Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar, inda Ya Gana Da Shugaban Kasar
Published: 2nd, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Alkahira
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi a yau Litinin.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya isa birnin Alkahira da yammacin jiya Lahadi domin tattaunawa da manyan jami’an kasar Masar.
A yayin wannan ziyara, Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi inda suka tattauna batutuwan baya-bayan nan a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da ci gaban yankin, musamman batun kalubalantar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu batutuwan kasa da kasa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da Shirin ministan harkokin wajen Iran na ziyartar ministan harkokin wajen kasar Masar da Lebanon a wani taron manema labarai da ya kira a yammacin ranar Asabar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ministan harkokin wajen harkokin wajen Iran kasar Masar
এছাড়াও পড়ুন:
Wata Kungiyar Ta Bukaci Shugaban Kasa Ya Cika Alkwarin Marigayi Shugaba Buhari Game Da Shehu Usman Aliyu Shagari
A wani roko da wata kungiya da aka fi sani da Sokoto Heritage Reloaded Initiative ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alkawarin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar.
An yi wannan roko ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a jihar Sokoto, inda shugaban kungiyar Farfesa Uthman Abdulqadir, ya jaddada muhimmancin girmama abubuwan da Shagari ya bari.
Ya tuna cewa shugaba Buhari ya yi wannan alkawari ne a ziyarar da ya kai Sokoto.
Farfesa Uthman ya bayyana irin rawar da Shehu Shagari yake takawa wajen ciyar da ilimi gaba a Najeriya, inda ya bayyana cewa ya taka rawa wajen aza harsashin kafa Budaddiyar Jami’ar Nijeriya.
Ya bayyana Shagari ba wai kawai shugaba ba, a’a a matsayin alama ce ta tawali’u, rikon amana da kishin kasa, mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa kasarsa hidima.
Farfesa Uthman ya bayyana kwarin guiwar cewa shugaba Tinubu, wanda ya shahara da mutunta shuwagabannin kasa da jajircewar hadin kai, zai gane muhimmancin tunawa Shehu Shagari.
Ya yi imanin cewa wannan aikin zai bayyana a fili karara Tinubu a matsayin jagora mai girmama kimar tawali’u, hidima, da kishin kasa.
Farfesa Uthman ya jaddada cewa sanyawa wurare sunayen Dattijai ba karamin alfanu ne ga rayuwa jama’ar ba.
Ya bayyana shi a matsayin muhimmin kayan aiki don ilimi, zaburarwa, da kuma kiyaye dabi’un da suka dace da al’ummomin yanzu da na gaba.
NASIR MALAL