Kasar Iran Ta Soki Rahoton Hukumar IAEA Na Baya-Bayan Nan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Published: 2nd, June 2025 GMT
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa, an shirya wannan rahoton ne karkashin tasirin wasu kasashen Turai.
A farkon taron manema labarai na mako-mako, Baghaei ya yi la’akari da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) da shahidan juyin juya halin Musulunci. Ya kara da cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar na ci gaba da gudanar da ayyukanta na bin diddigin batutuwan da suka shafi diflomasiyya, yana mai nuni da ziyarar da ministan harkokin wajen Iran ke yi a kasar Masar a halin yanzu, da ziyarar da zai kai kasar Lebanon gobe, da kuma gajeriyar ziyarar ministan harkokin wajen kasar Oman a birnin Tehran. Ya kuma bayyana ziyarar da mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya kai kasar Tajikistan domin halartar taron kasa da kasa, da kuma ziyarar shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran yake yi a kasashen Latin Amurka, inda ya jaddada cewa ayyukan sun hada da batun abubuwan dasuka shafi kasashen da na kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA