Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka

An gudanar da taron dandalin tattaunawa na masanan Sin da Afirka karo na 14 a birnin Kunming dake lardin Yunnan na kasar Sin a yau Talata, 20 ga wata, inda wakilai kimanin 100 daga Sin da kasashen Afirka fiye da 50 suka halarci taron tare da tattauna fasahohin mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa na kasar Sin da kasashen Afirka da kuma zamanintarwa irin ta kasar Sin.

Da yake tsokaci, Elia Kaiyamo, jakadan Namibia dake kasar Sin ya bayyana cewa, aikin zamanintar da kasa na da sarkakiya, domin kowace kasa tana da bambancin tarihi da al’adu da zamantakewar al’umma da tattalin arziki, don haka ya kamata a bi hanyoyi daban daban na zamanintarwa da suka dace da yanayin kasa, duk da cewa dukkansu suna da buri daya wato kyautata zaman rayuwar jama’a, da kawar da talauci, da raya zamantakewar al’umma mai inganci. Ya kara da cewa, fasahohin Sin na samun ci gaba sun shaida cewa, zamanintar da kasa tana da nasaba da bunkasuwar tattalin arziki, da sa kaimi ga samun daidaito a zamantakewar al’umma, da yi wa tsare-tsare kwaskwarima, da tafiyar da harkokin kasa yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaban kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin Ye Hailin ya bayyana cewa, a matsayinsu na kasashe masu tasowa, Sin da kasashen Afirka suna kokarin zamanintar da kansu don samar da gudummawa wajen zamanintar da kasashe masu tasowa a duniya, da kuma kyautata harkokin jama’ar duniya baki daya. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba
  • Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin
  • Sojojin Yemen Sun Kai Wa Filin Jirgin Saman “Ben Gorion” Hari Sau Biyu A Yau Alhamis
  • INEC Ta Samar Da Sashen Ƙirƙirarriyar Basira Domin Inganta Harkokin Zaɓe 
  • Dakarun Yemen Sun Hana Zirga-Zirgan Jiragen Sama A Filin Jirgin Saman Ben Gurion Na Isra’ila
  • Wasu ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaro Na Taimaka Wa Boko Haram – Zulum
  • Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan
  • Salon “Kasa Daya Manufa Daya” Ya Dace Da “Ayyuka Goma” Na Hadin Gwiwa Da Afirka
  • Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan
  • An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka