Da Ɗumi-ɗumi: Ana Fargabar Mutuwar Mutane Da Dama Yayin Da Tankar Mai Ta Fashe A Hanyar Zuwa Abuja
Published: 20th, March 2025 GMT
Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a hanyar Karu zuwa Nyanya dake birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da wata mummunar gobara da ta rutsa da motoci da dama, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a yammacin ranar Laraba. Har zuwa yanzu dai ba a tantance musabbabin fashewar tankar man ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jalali: Mun Hana Fitowar Sanadarorin Nukiliya Ta Hanyar Aiki Da Ka’idojin Tsaro
Shugaban hukumar tsaron ta fararen hula janar Jalali ya bayyana cewa; saboda aiki da ka’idojin tsaro sun yi nasarar hana fitowar sanadarorin Nukiliya da za su iya cuta da mutane.
Kamfanin dillancin labaru na “Mehr” ya nakalto janar Jalali yana cewa; Amurka ta kai hare-hare akan muhimman cibiyoyinmu da suke dauka cewa yana da girma da tsanani, sai dai mun dauki matakai na kariya da su ka hana fitowar sanadarori na Nukiliya da za su iya zama masu hatsari da cutarwa ga mutane.
Janar Jalali ya ce, tun a lokaci mai tsawo ne aka dauki wadannan matakan saboda kaucewa bacin rana.