Matatar Dangote Ta Dakatar Da Sayar Da Man Fetur A Naira
Published: 19th, March 2025 GMT
Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba. ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: man fetur a Naira
এছাড়াও পড়ুন:
Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi.
Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a ChinaUwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu.
Ana iya tuna cewa, tun a daren ranar 13 ga watan Yuni zuwa wayewar gari 14 ga watan ne aka kashe fiye da mutum 100 a ƙauyen Yelwata, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar.
Jihar Benuwe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma na ƙabilanci, wanda ke sanadiyyar salwantar rayuka da dama.