Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda
Published: 17th, April 2025 GMT
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita.
Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata.
Hakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: matatar man Dangote
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
Daga Bello Wakili
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu.
Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda shugabanni daga kasashen Afrika da sauran manyan baki daga sauran kasashen duniya za su halarta.
Shugaba Ouattara ya sake lashe zabe ne a ranar 25 ga watan Oktoban 2025, inda ya sake samu wani sabon wa’adi na jagorantar kasar. Sake Rantsar da shi na nuna da ci gaban da dimokuradiyya a kasar ta Côte d’Ivoire da kuma kyakkyawar dangantakarta da Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Kasar, halartar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima a taron na tabbatar da jajircewar Najeriya kan goyon bayan mulkin dimokiradiyya a yammacin Afrika. Najeriya na ci gaba da jaddada muhimmancin bin muradin jama’a da tabbatar da sauyin mulki cikin lumana a yankin.
Najeriya da Côte d’Ivoire na da kyakkyawar hulda ta aiki karkashin ECOWAS, Tarayyar Afrika, da kwamitin kasashe biyu, inda suke yin hadin gwiwa a fannoni irin su tsaro, kasuwanci, noma, yakar safarar mutane, da tattalin arzikin dijital. Dubban al’ummar ‘yan Najeriya da ke Côte d’Ivoire ma na kara zurfafa dangantakar tattalin arziki da al’adun kasashen biyu.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa zai koma Abuja bayan kammala taron rantsarwar.