Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja
Published: 9th, July 2025 GMT
Malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Hukumar Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) a babban birnin tarayya Abuja sun janye yajin aikin da suka tsunduma watanni uku da suka gabata.
Ana iya tuna cewa, tun a watan Maris ne dai malaman da ke ƙarƙashin ƙungiyar malamai ta ƙasa NUT suka tsunduma yajin aikin kan abin da suka kira rashin byan haƙƙoƙinsu na mafi ƙarancin albashi da aka ƙayyade na Naira dubu 70.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis din makon jiya ce Ministan Abuja, Nyesome Wike ya gana da shugabannin ƙungiyar malaman daga ƙananan hukomomi shida na Abuja da wasu masu ruwa da tsaki.
Bayan wannan ganawar ce gamayyar ƙungiyoyin malaman a yammacin wannan Talatar ta sanar da janye yajin aikin wanda ta ce zai fara ne daga gobe Laraba, 9 ga watan Yulin 2025.
Shugabannin ƙungiyoyin malaman da suka sanya hannu a takardar janye yajin aikin sun bayyana cimma wannan matsaya ce bayan sakin wani kaso da ya kai kusan naira biliyan 16 na bashin da za a biya malaman albashinsu na watannin da aka dokar sabon mafi ƙarancin albashin ta soma aiki.
Sanarwar ta ambato ƙungiyar malaman tana yi wa mambobinta godiya bisa haƙuri da jajircewa da kuma hadin kan da suka bayar tsawon lokacin da aka shafa ana yajin aikin.
Haka kuma, ƙungiyoyin malaman sun miƙa godiya ta musamman zuwa hedikwatar ƙungiyar malamai ta ƙasa NUT da ƙungiyar ƙwadago NLC reshen Abuja, da sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin fararen hula da duk wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin gwamnati ta waiwayi buƙatunsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: malaman firamare Yajin aiki janye yajin yajin aikin
এছাড়াও পড়ুন:
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp