Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da ’Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011, Inji Gwamna Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin daɗinsa na biyan bashin Naira Biliyan 13,944,039,204.64 da aka riƙe wa ’yan fansho a Zamfara tun daga shekarar 2011 zuwa 2023.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho tare da karbar rahoto daga kwamitocin haɗin gwiwa kan biyan bashin kuɗaɗen garatuti da aka yi a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, warware tarin bashin kuɗaɗen guratuti da fansho da aka tara daga shekarar 2011 zuwa 2023 na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin ta samu.

Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti.

Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60.

“Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na jiran a biya su haƙƙin su, Allah ya jiƙan su da rahama.

“Don magance wannan rashin adalci, mun kafa kwamitoci guda biyu domin su duba tare da ba da shawarar biyan duk wata garatuti da aka riƙe wa waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomi, a lokacin da muka karbi ragamar mulki shekaru biyu da suka wuce, duk da ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa, mun biya ma’aikatan gwamnati albashin watanni uku tare da biyan su alawus-alawus. Mun kuma daidaita alawus-alawus na alƙalai da ma’aikatan shari’a na tsawon shekaru.

“Mun daidaita duka waɗannan abubuwa. Lokacin da muka karbi mulki, mafi ƙarancin albashi a jihar ya kasance Naira 7,000.00 ne kacal, mafi ƙarancin albashi na N30,000, wanda aka amince da shi a shekarar 2019, gwamnatin da ta shuɗe ba ta taba aiwatar da shi ba, saboda sanin nauyin da ya rataya a wuyanmu, mun aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000.00 nan take.

“Bayan mun duba tsarin mafi ƙarancin albashin da ya ƙaru daga N30,000 zuwa N70,000.00 a watan Yulin 2024, mun aiwatar da sji bayan duk matakan da suka dace, ta yadda a cikin shekaru biyu na mulki, mun ƙara mafi ƙarancin albashi a jihar daga N7,000.00 zuwa N70,000.00.

“Bugu da ƙari kuma, mun bullo da kuma aiwatar da hanyoyin kyautata wa ma’aikata a yayin bukukuwan Sallah da kuma ƙarin garabasar albashin ƙarshen shekara, wanda aka fi sani da albashin wata na 13 ga duk ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman gwamnati, ba a taba yin hakan ba a tarihin jihar.

“Sakamakon biyan kuɗaɗen garatuti ya ƙara wa ma’aikata kwarin gwiwa tare da dawo da amincewar jama’a kan harkokin mulki, za mu ci gaba da tabbatar da samar da kuɗaɗen fansho cikin gaggawa, domin yin hakan, gwamnatin jihar a shirye take ta haɗa gwiwa da ƙungiyoyin ‘yan fansho domin tafiya daidai da sauye-sauyen da muka yi.

“Yayin da nake samun wannan rahoton, ina so in yaba wa ƙoƙari da jajircewar ‘yan kwamitin, wannan ba abu ne mai sauƙi ba, ina sane da ƙalubalen da ‘yan kwamitin suka fuskanta a yayin gudanar da aiki, ba yaba da jajircewarsu.

A yayin ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da yin garambawul a harkokin fansho na jiha da ƙananan hukumomi.

“Gwamnatina ta kafa wani kwamiti da zai duba ayyukan da suka gabata na hukumar fansho a jihar, kwamitin ya kammala aikinsa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a ci gaba, wani bangare na shawarwarin shi ne kafa kwamitin aiwatar da ayyukan fansho.

“Don bin tsarin Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Fansho ta Jiha, da duk masu ruwa da tsaki za su duba tare da sabunta dokar fansho ta Jihar Zamfara domin Majalisar Dokokin Jihar ta amince da ita cikin gaggawa.

Aminu Dalhatu/Gusau

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zamfara mafi ƙarancin albashi da suka yi ritaya

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindigar Da Suka Zo Sace Wani Ɗan China

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin. An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan.

CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China

Majiyar ta ce haɗin gwuiwar jami’an Soja, da ‘yansanda, da masu farauta da ‘yan bijilanti sun bi sawun maharan cikin dazuka, lamarin da ya tilasta su bar ɗan ƙasar China da suka sace. “Har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a dazukan yankin don kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika,” in ji ta.

Kakakin Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya ce yana jiran cikakken rahoto daga DPO na yankin kafin ya bayar da ƙarin bayani. Majiyar ta kuma buƙaci a ƙara yawan jami’an tsaro a yankin da sauranɓm ɓɓ wuraren da ake fargabar barazanar tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni
  • ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni
  • ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sa-kai Sama Da 70 A Filato
  • Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
  • Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindigar Da Suka Zo Sace Wani Ɗan China
  • Malamin Addinin Musulunci Yayi Kira Da Ayi Gaggawa Gyaran Hanyar Zamfara
  •  Nijar: An Kashe Sojoji 10 A Wasu Hare-hare Biyu Na ‘Yan Ta’adda
  • Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC