Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin Tarayya Wutar Lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Tabbatar da Yunkurin Kafa Cibiyar Tarayya Ta Uku a Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma.

Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse.

Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci.

Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa  mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani.

“Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne mai sauƙi. Kun shiga tarihin wannan kwaleji, wacce idan ta yi nasara, za a tuna da ku cikin alheri; idan ta gaza kuma, babu shakka hakan zai shafe ku. Amma ina da tabbaci, ganin irin mutanen da ke cikin wannan tawaga, cewa kwalejin ta fara da ƙafar dama,” in ji shi.

Namadi ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da dokokin da suka kafa Kwalejin Noma ta Tarayya a Kirikasamma da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Birnin Kudu, inda ya bayyana cewa Jigawa na kan hanyar samun wata cibiyar tarayya ta uku bayan tattaunawar da ya yi da shugaban ƙasan.

Gwamna Namadi ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga tawagar gudanarwar.

 

“Za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da nasarar fara aiki a kwalejin, kuna da cikakken goyon bayanmu, mun yi sa’a sosai da samun Dr. Gwaram a matsayin jagoran wannan cibiyar, ƙwararren masani a fannin noma, gogaggen mai gudanarwa, kuma ɗan asalin Jigawa mai kishin ƙasa.”

Ya yaba wa Ministan Noma, Ministan Ilimi, da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Birniwa/Guri/Kirikasamma, Alhaji Fulata, kan rawar da suka taka wajen ganin an kafa sabuwar kwalejin.

Haka kuma ya jinjinawa shugaban kwalejin da Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu bisa jajircewarsu.

Tunda farko, shugaban kwalejin, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa goyon bayanta, tare da jaddada cewa kwalejin ta shirya fara aiki nan take.

A cewarsa, kwalejin za ta kasance cibiya ta musamman da za a koyar da ingantattun hanyoyin noma na zamani.

Ya bayyana cewa sun shirya horas da manoma da kuma jawo hukumomin da suka dace zuwa Jihar Jigawa.

Ya ce sun fara tattaunawa da hukumomin da ke da alhakin rajista da tsari kamar NBTE da sauran da ake buƙata don fara aiki.

Ya yaba da irin  ƙoƙarin da aka yi wanda ya kai ga amincewa da kafa cibiyar, yana mai jaddada yawan tattaunawar da aka yi da hukumomin tarayya, masu tsara doka, da masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar wa gwamna cewa tawagarsu za ta yi aiki tukuru wajen cimma nasara kwalejin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki
  • Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana
  • Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar
  • Gwamna Namadi Ya Tabbatar da Yunkurin Kafa Cibiyar Tarayya Ta Uku a Jigawa
  • Jihar Jigawa Ta Amince da Naira Biliyan 3.5 a Matsayin Kudaden Tallafin UBEC 2025
  • Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas
  • NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki