Iran Ta Kira Jakadun Kasashen Jamus da Butaniya Zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje Don Jan Kunnensu
Published: 20th, March 2025 GMT
Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta Iraki.
Sannan ta bayyana yadda kasar Burtania ta dade tana adawa da JMI, daga ciki har da goyon bayan da kasashen biyu suke bawa HKI a kissan kiyashin da take wa falasdinawa a gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Yahudawan Iran Ya Tuhumi Isra’ila Da Fakewa A Karkashin Addini
Shugaban yahudawan Iran Rabbi Younes Hamami Lalezar ya ce, Isra’ila tana amfani da addini yahudanci domin cimma manufofinta, tana kuma bayyana Iran a matsayin wacce take fada da addinin yahudanci,alhali a cikin iran da akwai zaman lafiya tsakanin Mabiya dukkanin addinai.
Haka nan kuma ya ce, kiyayyar da Isra’ila take da shi akan Iran ne, yake sa take jinginawa Iran din kin jinin yahduawa,wanda aikin ‘yan sahayoniya ne su samar da rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran bisa addini da kuma kabila.
Isra’ila tana bayyana kanta a matsayin mai bai wa yahudawa kariya, sai dai da dama daga cikin Mabiya addinin yahudanci, wadanda ba ‘yan sahayoniya ba, suna zarginta da amfani da addini saboda manufofi na siyasa.
Fiye da shekaru 2,700, yahudawa suke rayuwa a cikin Iran,kuma suna da wuraren bautarsu da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsangwama ba.
Rabbi Younes Hamami Lalezar ya kuma ce: A Iran, yahudawa suna aiki, suna yin bautarsu, da rayuwa a ko’ina, suna da dakunansu na ibada -Synagogues- a cikin sauki da ‘yanci ba tare da wata kariya ta jami’an tsaro kamar yadda yake a cikin kasashen turai ba.
Haka nan kuma ya ce, yadda muke rayuwa ta girmama juna a tsakanin musulmi, yahudawa, da kiristoci, shi ne babban abinda yake bayyana hakikaninmu, don haka duk wani zargi na kin jinin yahudawa ba shi da madogara.”