Amurka Tana Fatan HKI da Hamas Su Tsaida Budewa Juna Wuta Na Kwanaki 60 A Karshen Wannan makon
Published: 9th, July 2025 GMT
Jakadan Amurka na musamman a yankin yammacin Asiya Steven Witkoff ya bayyana cewa yana fatan HKI da kuma kungiyar Hamas zasu cimma yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta a karshen wannan makon.
Jakadan ya kara da cewa idan har yarjeniyar ta tabbata, kungiyar Hamas zata mikawa HKI yahudawa masu rai 10 da kuma gawakinn wasu 09 .
Steven Witkoff bai bayyana abinta ita Hamas da kuma sauran Falasdinawa zasu samu a wannan yarjeniyar na kwanaki 60 ba. Musamman bayan ta rasha falasdinawa kimani 57500 ya cikin watanni kimani 21 yahudawan suna fafatawa da ita ba.
Har’ila yau falasdinawa 150,000 suka ji rauni mafi yawansu mara da yara. A cikin wadanda aka kashe akwai yara kimani 12, 000
Daga karshe Witkoff, yace a halin yanzu sabani guda ne kacal ya rage ba’a warware ba, cikin guda hudu da ake tattaunawa da Hamas na lokaci mai tsawo.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.