HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni
Published: 9th, July 2025 GMT
Wani babban jami’I a kungiyar Hamas ya bayyana cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa guda 6 a zirin gaza a ci gaba kissan kiyashin da takewa falasdinawa a yankin.
Abdul-Karim Hanini, ya kara da cewa wadanda ta kashen tsoffin fursinoni a hannun yahudawan a shekarun da suka gaba 5 daga cikinsu an yi musayarsu ne a shekara 2011 a lokacinda aka yi musayarsu da fursinan yahudawan Galid Shalit a shekarar.
Abdul-Karim Hanini ya kammala da cewa a dai dai lokacinda muke makokin yan’uwammu da yahudawan suka kai ga shahata, muna rokon All..ya karbi shahadarsu, sannan muna kara nanata cewa zamu ci gaba da gwagwarmaya da su har zuwa jinni na karshe da zamu iya zubarwa ko kuma mu sami nasara a kansu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen
Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen.
Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa da kuma Salif, wani sabon laifi ne na ha’inci da ya kara yawan muggan laifukan ‘yan mamaya a yanki.”
Sanarwar ta kara da cewa: Wannan mummunan wuce gona da iri na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Yemen da dakarunta ke samun nasarori a jere wajen karya martabar makiya ‘yan sahayoniyya da kutsawa cikin zurfin dabarun na yaki da kuma kafa madaidaicin matakin da ya dace wanda ke nuna ‘yancin kai na mutanen da ba su san yadda za su ja da baya ba.