Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe
Published: 20th, March 2025 GMT
Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira.
Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin sake farfaɗowa daga wannan masifa.
Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus.
Hukumomin yankin har zuwa yanzu ba su bayyana ainihin dalilin tashin gobarar ba, yayin da waɗanda abin ya shafa suke zaune ba tare da matsuguni ko abinci ko kayayyakin amfani na yau da kullum ba.
Malama Sakina, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, cikin kuka tana mai bayyana cewa, “Mun rasa komai. Babu wanda ya taimaka mana lokacin da gobarar ta tashi. Muna buƙatar taimako, musamman daga gwamnati da masu taimakon jama’a, domin mu sake tsayuwa. Kowa ya san halin ƙunci da ake ciki yanzu.”
Wani wanda gobarar ta shafa, Yakubu Baba Gombe, ya bayyana damuwa kan jinkirin da jami’an kashe gobara suka yi wajen isowa wurin. inda ya ce, “Lokacin da suka iso, komai ya riga ya ƙone.”
Iyalan da abin ya shafa yanzu haka sun dogara ne ga taimakon al’umma don samun tallafi na gaggawa. A halin yanzu kuma, mazauna yankin suna kira ga hukumomi da su gudanar da bincike kan lamarin tare da ɗaukar matakan kariya daga aukuwar irin wannan gobarar a nan gaba.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin ya ji ta bakin hukumar kashe gobara kan wannan gobarar amma lamarin ya citura
Wannan iftila’i ya bar mutane cikin baƙin ciki, yayin da iyalai ke roƙon taimako domin sake gina rayuwarsu. Ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara bai yi nasara ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: tashin gobara da abin ya shafa
এছাড়াও পড়ুন:
Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
Marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya ce kamata ya yi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tura ɗansa, Seyi Tinubu, zuwa Jamhuriyar Benin domin “kwantar da” yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba.
Soyinka ya soki matakin Tinubu na tura dakarun rundunar Sojojin Sama ta Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi domin kifar da Shugaba Patrice Talon daga mulki.
Ya yi wannan jawabi ne a bikin bayar da kyaututtuka na shekara karo na 20 da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a Legas ranar Litinin.
Fitaccen marubucin ya tuna yadda ya ga jami’an tsaro masu makamai sosai suna gadin Seyi Tinubu a Legas.
Ya ce: “Shugaba Tinubu bai kamata ya tura Sojojin Sama da na ƙasa ba domin shawo kan wannan tayar da hankali da ke barazana ga tsaronmu da daidaituwarmu; a’a akwai hanyoyi mafi sauƙi na yin hakan.
“Bari in gaya muku inda Tinubu ya kamata ya nemi rundunar da za ta shawo kan wannan tayar da hankali, na nan a Legas ko ma a Abuja, amma babu buƙatar kiran sojojin ƙasa ko na sama.
“Zan gaya muku abin da ya faru a ɗaya daga cikin ziyarata zuwa gida watanni biyu da suka gabata, ina fita daga wani otel sai na ga abin da ya yi kama da wurin yin fim, wani matashi ya rabu da ’yan wasan ya zo ya gaishe ni cikin ladabi.
“Na kalli wurin sai na ga kusan rundunar sojoji ce gaba ɗaya sun mamaye filin otel ɗin a Ikoyi. Na koma cikin motata na tambaya wanene wannan matashin, sai aka gaya min.
“Na ga sojoji, haɗin jami’an tsaro masu makamai sosai, akalla 15 suna ɗauke da manyan makamai, abin da ya isa ya tsare karamar makwabciya kamar Benin.
“Na yi tunanin cewa a gaba mai girma shugaban ƙasa ya kamata kawai ya kira ya ce ‘Seyi je ka kwantar da fitina a can’. Na yi matuƙar mamaki har na fara neman Mashawaracin Shugaban Kasa a fannin tsaro,” in ji Soyinka.
Soyinka ya kuma ce ba Tinubu ne shugaban da ya fara mulkar Najeriya yana da ’ya’ya ba, don haka bai ga dalilin da zai sa a girke tarin jami’an tsaro kawai don su rika gadin dansa ba.