Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Godewa JMI Dangane Da Tallafawa Kungiyar Saboda Gwagwarmaya Da HKI
Published: 9th, July 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya godewa shugabancin JMI, wato Imam Sayyif Aliyul Khaminaei kan goyon bayan da yake bawa kungiyar babu kakkautawa don yakar makiyar kasar HKI.
Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon, a karon farko tun bayan shahadr shugaban kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah a shekarar da ta gabata.
Babban malamin ya kara da cewa, taimakon da Imam Khaminae yayiwa kungiyar Hizbullah, ya kai matsayinda ba zamu tambaya, ko roka ba. Musamman bayan fara yaki a cikin watan Octoban shekara ta 2023, kuma ta bada wadannan taimakon ba tare da ta shiga yakin kai tsaye ba.
Sheikh Qasem ya bayyana cewa, bamu bukaci JMI ta shiga yakin ba, kuma bai kamata ta shiga yakin ba, saboda muma bama bukatar da shiga yakin.
Daga karshen shugaban kungiyar ya bayyana cewa zancen da aka cika duniya da shin a cewa kungiyar ta mika makamanta ga gwamnatin kasar. Saboda takurawar da manya-manyan kasashen duniya suke yi don shi ne bukatar HKI.
Don haka yamata su san cewa bamu da Kalmar mika kai a kamusimmu, ko nasara ko shahada babu wata na uku iji shi.
Kuma wannan halin da ake ciki, na keta hurimun yarjeniyar 1701 wanda HKI take yi ba zai dore har’abada ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: shiga yakin
এছাড়াও পড়ুন:
Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza
Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi.
Shafin labarai na Isra’ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da matsaloli masu alaƙa da damuwa da kuma rasa abokai biyu a yaƙin na Gaza.
Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a BornoTRT ya ruwaito cewa an gano gawar sojan a cikin wani daji kusa da birnin Safed a arewacin Isra’ila bayan ya kasa samun sukuni da yadda zai yi ya magance damuwar da ya shiga.
“Ba zai iya jurewa ba kuma ya koka da ganin hotunan gawawwaki da kuma jin warin mutuwa a kullum,” in ji mahaifiyarsa.
A cewar kafafen yaɗa labarai na Isra’ila, adadin sojojin da suka kashe kansu ya ƙaru tun bayan ɓarkewar yakin Gaza a watan Oktoban 2023.
Wani rahoto daga jaridar Israel Hayom ya nuna cewa sojoji 21 sun kashe kansu a shekarar 2024.
A watan Mayu, jaridar Haaretz ta Isra’ila ta ce sojoji 42 sun kashe kansu tun bayan ɓarkewar yakin Gaza.
Duk da kiran duniya na tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza, inda ta kashe fiye da mutum 57,400, yawancinsu mata da yara, tun daga watan Oktoban 2023.