Matashi ya kai kansa ofishin ’yan sanda
Published: 16th, April 2025 GMT
Wani matashi, Umar Auwal, mai shekaru 20 da ya yi iƙirarin kashe mutane ya miƙa kansa ga rundunar ’yan sanda a Jihar Kano.
Matashin mai inkiyar ‘Abba Dujal’ ya ce ya miƙa kansa ga mahukunta ne sakamakon rashin samun kwanciyar hankali tun bayan ta’addancin da ya aikata a bayan nan.
Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — GandujeHakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon murya da kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Da yake amsa tambayoyi, Abba Dujal ya yi iƙirarin aikata manyan laifuffuka da suka haɗa da kisan kai, fashi da makami da kuma satar babur da wayoyin hannu.
Matashin ya yi iƙirarin kashe wani mutum mai suna ‘Boka’ a unguwar Sabon Gari ta Kano, inda ya sace wayarsa Infinix Hot 40i, ya kuma sayar da ita a kan N40,000.
Haka zalika, ya bayyana yadda ya kashe wani mutum a unguwar Kurna da ke Kano, inda ya arce da wayarsa ƙirar Samsung S26 da ya sayar a kan N160,000.
A Jigawa kuwa, ya ce ya kashe wani mutum a karamar hukumar Ringim tare da sace babur ɗinsa da ya sayar da shi a kan N300,000.
Abba Dujal ya ce yanzu haka ya shekara bakwai bai yi sallah ba. Sai dai ya ce an saka shi a Islamiyya amma malamin ya dawo da shi gida saboda fitinar da yake a makarantar.
A fannin karatun boko kuma, Abba Dujal ya ce ya taɓa shiga firamare amma daga nan bai ƙara gaba ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Lukurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato
Wasu ‘yan bindigar da ake zargi Lukurawa ne a wani sabon hari sun kashe mutane sama da 15 a Qaramar Hukumar Tangaza ta jihar Sakkwato, ranar Litinin da ta gabata.
Babban Jami’i a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Qasa(Red Cross) reshen Sakkwato Alhaji Abubakar Ainu ya tabbatar wa Aminiya harin wanda ya yi matuqar tayar da hankalin mutanen yankin ganin an xauki dogon lokaci kafin kawo irin wannan hari mai muni.
Ainu ya ce, “jami’anmu na sa kai sun ziyarci qauyen Kwalajiya na mazabar Magoho a garin Tangaza domin jajantawa da kuma halartar sallah janaza ta muanen da ‘yan bindigar suka kashe sama da 15. Waxanda suka jikkata an kai su Asibitin Kashi na Wamakko da Asibitin Koyarwa ta Xanfodiyo da na Qwararru a birnin jiha domin karvar magani.”
Ya ce yankin na cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro ta varayin shanu da masu tayar da qayar baya.
“Wannan lamari baya da daxi ko kaxan, dubi yadda aka mayar da wasu mata zawarawa aka mayar da wasu yara marayu domin biyan wata buqata wadda addini bai yarda da ita ba, ina kira ga hukuma ta sake salon yaqar ‘yan bindiga da take yi,” in ji Ainu.
Wani mazauni qauyen Kwalajiya ya ce ‘yan bindigar Lukurawa sun zo a qauyen a daren Lahadi har zuwa Asuba ta ranar Litinin in da suka kashe wasu mutane a harin da suka kai, a lokacin da suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
“Bayan sun kashe mana mutane sun tafi da dabbobi masu yawa, duk da mutanenmu sun yi qoqari amma yawan mutane da makaman da suke xauke da su ya sa suka fi qarfinmu. Har zuwa yanzu ba mu san adadin waxanda aka kai asibiti ba domin suna da yawa, sai dai waxanda suka rasu 15 muka yi wa Sallah.
“Muna kira ga jami’an tsaro su mayar da hankali wurin korar mana waxannan ‘yan bindigar don mu samu zaman lafiya a jiha baki xaya.”