Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.

 

Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba.

 

“Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta ne, amma ‘yan Nijeriya sun damƙa wa Shugaba Tinubu wata gagarumar amanar sauyi, wadda aka gina bisa Shirin Sabunta Fata,” inji shi.

 

A cewar sa, shekaru biyu kacal bayan hawan Tinubu mulki, gwamnatin ta fara samun gagarumin cigaba a fannonin tattalin arziki da tsaro inda ake samun raguwar satar ɗanyen mai, hauhawar farashin kaya na raguwa, Naira na daidaita, da kuma ƙarin ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren man fetur da gas.

 

“Fasa bututun man fetur ya ragu ƙwarai, ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren man fetur da gas na dawowa, hauhawar farashin kaya na raguwa, Naira na samun daidaito, ana fuskantar matsalolin tsaro kai-tsaye, kuma miliyoyin ‘yan Nijeriya — iyalai, ɗalibai, masu aikin hannu, da ‘yan ƙananan sana’o’i — na amfana daga shirye-shirye irin su lamunin karatu, samun bashi na kayayyakin masarufi, sauya motocin haya zuwa masu aiki da iskar gas, da ingantattun ayyukan gwamnati da ababen more rayuwa,” inji Ministan.

 

Ya kuma bayyana wasu muhimman matakai da aka ɗauka kwanan nan, ciki har da rattaba hannu kan dokoki huɗu na gyaran haraji da za a fara aiwatar da su daga shekarar 2026, da kuma ƙaddamar da mafi girman shirin amfani da injuna a aikin gona da aka taɓa yi a Nijeriya.

 

“Makonni biyu da suka wuce, Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu kan dokoki huɗu masu muhimmanci na gyaran haraji, wanda ke zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin kuɗi da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya. Ana sa ran waɗannan gyare-gyare za su haɓaka walwala da cigaban iyalai da ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar nan,” inji shi.

 

“Kafin hakan, Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da mafi girman shirin amfani da injuna a aikin gona da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya — wanda ya kasance fara aiwatar da Shirin Sabunta Fata na amfani da injuna a aikin gona. Wannan kuwa yana daga cikin jerin manyan shirye-shiryen amfani da injuna a aikin gona da ake aiwatarwa domin tabbatar da wadatar abinci,” inji shi.

 

Ministan ya zargi wasu ‘yan siyasa da ƙoƙarin dagula hankali domin a ɗauke hankalin gwamnati daga cigaban da ake samu. Ya ce gwamnati ba za ta amince da hakan ba.

 

“Ba abin mamaki ba ne cewa sababbin haɗakar siyasa da ƙungiyoyin adawa ba sa son a ci gaba da maida hankali kan irin cigaban da Nijeriya take samu. Sai dai gwamnati ba za ta bari a jawo ta cikin hayaniyar da waɗanda ke son Nijeriya ta tsaya cak maimakon ta ci gaba da samun sauyi suka ƙirƙira ba,” inji shi.

 

A ƙarshe, Idris ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da ƙudirin ta na inganta rayuwar al’umma.

 

Ya ce: “Gwamnatin Tinubu tana maida hankali sosai tare da jajircewa wajen gina Nijeriya mai wadata ga kowa da kowa.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya 

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu.

Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC

Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.”

Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne.

“Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna mayar da yara marayu ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba,” in ji shi.

Tinubu, ya kuma sha alwashin ci gaba da inganta walwalar sojoji da ba su kayan aiki na zamani.

“Za mu ci gaba da zuba jari a makamai, bayanan sirri da horo. Sojojinmu dole su kasance a shirye a koyaushe don kare Najeriya.”

Ya jinjina wa sojojin da suka rasa rayukansu wajen kare ƙasa.

“Jininsu ba zai zube a banza ba. Za mu ci gaba da tunawa da su har abada.”

Shugaban Hafsan Soji, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa jarumtar dakarun sojin Najeriya.

“Karfinmu na gaske shi ne jarumta da sadaukarwar sojan Najeriya,” in ji shi.

Bikin ya ƙayatar da dandazon jama’a da manyan baƙi, inda aka nuna kayan aikin dakarun na zamani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi: Ana Kokarin Rubuta Sabon Babi Na Zamanantar Da Sin A Lardin Shanxi
  • ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’
  • Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC
  • ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027
  • Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko
  • Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
  • Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya 
  • Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala