Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
Published: 9th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Amurka da JMI sun lalace ne saboda zagon kasar HKI da farwa kasar da yaki. Yace gwamnatin Amurka idan tana so zata farfado da shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani rubutun da yi wa jaridar ‘Financial Times ta Amurka.
Sai dai, inji ministan, yakamata Amurka ta san cewa al-amura sun sauya kuma bayan wannan yaki na kwanaki 12 da HKI da ita suka kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar har guda uku ta kuma kashe manya-manyan Janaral na sojojinmmu sannan ta kashe masana fasahar nukliyammu da kuma wasu Iraniyawa.
Aragchi ya ce: Iran ba zata mika kai kamar yadda Amurka take riyawa ba. Iran kasashe wacce tayi shekaru dubbai a duniya, kuma ta kutsa yake-yake da dama a baya ta kuma sami nasara. Sannan yace: Muna son zaman lafiya a ko yauce, amma mune muke iya tabbatar da ita ko mu hanata tabbata.
Yace: A halin yanzun kuma ba zamu taba amincewa da kissam mutanemmu ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil.
An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya.
Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da kuma Amurka ya sabawa dikokin kasa da kasa sannan ko wane bangare yana da rawar da zai take don ganin an tabbatar da zaman lafiya a duniya.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yace: hare-hare kan kasar Iran musamman a kan shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya abin yin tir da shi ne. Sannan ya kara da cewa kasar Rasha a shirye take ta taimaka ko a fagen kwamitin tsaro na MDD ne.