Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta cafke mutane biyu da ake zargi da satar babura wadanda ta ƙwato babura biyu a hannunsu hadi da wani wanda aka tsinta a lokacin sintiri.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an gudanar da samamen ne bisa bayanan sirrin da aka samu daga wani mai kishin ƙasa, wanda ya kai jami’an Operation Hattara har zuwa wata maɓoyar ɓata gari a Tudun Hayin Kwarin-Misau, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akko
An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a Nijeriya An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a KebbiRundunar ta ce an kama Misba’u Adamu mai shekaru 25 dan asalin garin Alkaleri na Jihar Bauchi da Adamu Ibrahim mai shekaru 28, daga Karamar Hukumar Garko ta Jihar Kano.
A lokacin binciken, waɗanda ake zargin sun amsa laifin satar babura guda biyu a gidan wani Mohammed Usman da misalin karfe 4 na Asuba a ranar 6 ga Yuli, 2025.
Baburan sun haɗa da Qlink Cassie mai lamba ABC 484 WN da Hero Hunter mai lamba GME 36 QL.
A sanarwar, rundunar ’yan sandan ta kiyasta darajar baburan kan Naira miliyan 1.8 wadanda aka gano a gidan wani abokin huldarsu da ake kira Babangida.
A wani labarin na daban, rundunar ta ce wani mutum ya tsere ya bar babur kirar Jincheng Kasea mai lamba DKU 099 UK a Wuro Birji yayin da ‘yan sanda ke sintiri da misalin karfe 1 na dare.
Rundunar ta ce tana ci gaba da kokarin gano masu laifin da kuma mamallakin babur ɗin da aka tsinta.
Ta kuma jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kira da su ci gaba da ba da bayanai masu amfani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babura Barayi jihar Gombe
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi
Wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta samu nasarar kuɓutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su da shanu da aka sace a Jihar Kebbi.
Bayanai sun ce an sace mutanen da dabbobin ne a ƙauyukan Ukuhu da Kokanawa a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar.
‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’ Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADCWani daraktan tsaro a Gwamnatin Kebbi, Abdurrahama Zagga ne ya sanar wa manema labarai nasarar da aka samu a ranar Talata, inda ya ce an kai samamen ne bayan umarni da aka samu daga Gwamna Nasiru Idris bisa bayanan sirri da aka tattaro a yankin.
A cewar Zagga, tawagar jami’an tsaro ta fatattaki ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da mutanen da kuma shanun da suka sace a wani gulbi da ke iyaka da Jihar Zamfara.
“Mutane da aka ceto an mika su ga iyalansu. Kuma wannan abin farin ciki ne ga gwamna musamman a kokarin da jami’an tsaro suke yi, lamarin da zai kara inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin masarautar Zuru.”
Ya bayyana fatan da suke da shi na kawar da ɓarayin shanu da ’yan bindigar Lukurawa a yankin Zuru da Argungu.