Dakarun Qassam sun harba makami mai linzami a kan Tel Aviv
Published: 20th, March 2025 GMT
Dakarun Falasdinawa sun mayar da martani ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa fararen hula bayan sake dawo da yakin Isra’ila a kan al’ummar Gaza, inda suka harba rokoki zuwa Tel Aviv.
Al-Qassam Brigades, reshen soji na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas, ta sanar a wannan Alhamis cewa, ta yi ruwan makamai masu linzami samfurin M90 a kan birnin Tel Aviv, a matsayin mayar da martani ga kisan kiyashi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi kan fararen hula a zirin Gaza.
Sojojin mamaya na Isra’ila sun tabbatar da cewa sun gano wasu rokoki guda uku da aka harba daga Gaza zuwa tsakiyar Falasdinu da suka mamaye, tare da jin karar makamai a sararin samniyar Tel Aviv, Gush Dan, da matsugunan yahudawa da ke kewaye.
Isra’ila bat a mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, kamar yadda ta yi fatali da mataki na biyu na yarjejeniyar , tare da sanya wasu sharudda da gangan domin matsin lamba a kan kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu.
Isra’ila Ta sake sabunta kai hare-hare a zirin Gaza, inda ta kai hari a wurare daban-daban na yankin tun daga kwanaki biyu zuwa uku da suka gabata har zuwa yau.
Hare-haren na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun yi sanadin shahadar daruruwan fararen hula, galibi mata da kanan yara, tare da jikkata wasu da dama .
Wakilin Al-Mayadeen ya tabbatar da cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake raba arewacin Gaza daga tsakiya da kuma kudancin yankin, inda suka sake kwace iko da yankin Netzarim.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Adadin Wadanda Su ka Kwanta Dama A Gobarar Tashar Jirgin Ruwan Shahid Raja’i Sun Kai 21
Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14.
Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21
Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa rayukansu za a mika su ga iyalansu domin yi musu jana”iza.
Biyu daga cikin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu, mata ne sauran kuma maza ne.
A jiya Asabar ne dai aka sami fashewa mai karfi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’i da hakan ya yi sanadiyyar jikkata da kuma mutuwar mutane da dama.
Tuni aka bude bincike domin gano musabbabin abinda ya faru.