OIC ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren yahudawan sahyuniya a kan a zirin Gaza
Published: 20th, March 2025 GMT
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka.
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan ya saba wa dukkanin dokokin kasa da kasa.
Ya kuma jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wannan kisan kiyashi da mashinan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da fararen hula.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yi Allah wadai da
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
Bayan duguwar tattaunawa a birnin Istanbul na kasar turkiya kasashen pakisatan da Afghanistan sun amince da batun tsawaita dakatar da bude wuta a tsakanin iyakokin kasashen, bayan da kasashen turkiya da Qatar suka shiga tsakanin domin samun daidaito.
Gwabzawa a iyakokin kasashen biyu dake mukwabtaka a yan makwannin nan yana barazana sosai ga zaman lafiyar yankin, sai dai wannan yarjejeniyar za ta hana yaduwar fadan da kuma kara samun hadin guiwa kan tsaron iyakokin.
Zabiullah mujahid kakakin kungiyar Taliban ya tabbatar da kulla yarjejeniyar, kuma yace Kabul tana son samun kyakkyawar dangantaa da dukkan kasashen dake makwabtaka da ita, musamman kasar Pakistan bisa mutunta juna da kuma rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci