HausaTv:
2025-07-09@11:20:51 GMT

Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda

Published: 9th, July 2025 GMT

Tsohon babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci wato IRGC ya bayyana cewa a yakin da JMI ta fafata a cikin watan da ya gabata , ya tabbata cewa JMI tana iya yaki da Amurka da HKI a lokaci guda.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Mohsen Rezaei, yana fadar haka a lokacinda wata talabijin ta cikin gida take hira da shi a jiya Talata .

Labarin ya kara da cewa Janar Rezaei ya taba rike mukamin babban kwamandar rundunar IRGC jim kadan bayan nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979.

Yace: Shahid Janar Qasem Sulaimani, Babban kwamandan rundunar Qudus ne  ya fara furta zancen cewa , Iran tana da karfin fuskantar Amurka. Wannan kuma ya tabbata a yankin kwanaki 12 da aka dorawa kasar.

A halin yanzu dai Janar Rezaei yana cikin wadanda suke bawa Jagoran juyin juya halin musulunci shawara a kan al’amuran tsaro da siyasa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta

Kakakin hafsan hafsoshin sojojin Iran ya ce; Iran tana dora wa Amurka  alhakin duk wani hari da za a kai mata

Kakakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Birgediya Janar Abul-fazl Shekarchi ya jaddada cewa: Iran tana dorawa Amurka alhakin duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta.

A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Shekarchi ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran ba su ne suka kaddamar da harin kan wata kasa ba, amma sun mayar da martani cikin kwanaki 12 na arangama da munanan hare-hare da suka fuskanta daga mabartan ‘yan sahayoniyya makiya.

Ya kara da cewa, “An sanya wa makiya tsagaita bude wuta ne bayan da suka fuskanci munanan hare-hare daga sojojin Iran,” yana mai cewa, “Iran sakamakon karfin martanin sojojinta ne ta tilastawa makiya dakatar da yakin, ba kamar yadda suke ikirari ba, cewa su ne suka dakatar da yakin a kashin kansu, sannan kuma Iran ce karshen wacce ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka ciki kan mabarnata ‘yan sahayoniyya.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliya Kasar Idan Tanaso
  • Iran Za Ta Yi Nazarin Sabuwar Gayyatar Da Amurka Ta Yi Mata Na  Sabuwar Tattaunawa
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
  • HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
  • Amurka Ta Soke Dokar Da Ta Tabbatar Da Hai’at Tarirusham Cikin Jerin Kungiyoyin Yan Ta’adda
  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza