Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki
Published: 9th, July 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.কীওয়ার্ড: Firamare Yajin Aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu.
Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APCTinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.”
Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne.
“Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna mayar da yara marayu ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba,” in ji shi.
Tinubu, ya kuma sha alwashin ci gaba da inganta walwalar sojoji da ba su kayan aiki na zamani.
“Za mu ci gaba da zuba jari a makamai, bayanan sirri da horo. Sojojinmu dole su kasance a shirye a koyaushe don kare Najeriya.”
Ya jinjina wa sojojin da suka rasa rayukansu wajen kare ƙasa.
“Jininsu ba zai zube a banza ba. Za mu ci gaba da tunawa da su har abada.”
Shugaban Hafsan Soji, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa jarumtar dakarun sojin Najeriya.
“Karfinmu na gaske shi ne jarumta da sadaukarwar sojan Najeriya,” in ji shi.
Bikin ya ƙayatar da dandazon jama’a da manyan baƙi, inda aka nuna kayan aikin dakarun na zamani.