Hamas ta ce a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage, domin musanya fursunoni”
Published: 14th, April 2025 GMT
Wani babban jami’in Hamas ya ce kungiyar a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage a zirin Gaza da aka yi wa kawanya, domin musanya abin da ya bayyana da ” fursunoni” da kuma tabbatar da kawo karshen yakin kisan kare dangi da ake ci gaba da yi.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto Taher al-Nunu na cewa: “A shirye muke mu sako dukkan ‘yan Isra’ila da ake tsare da su a yarjejeniyar musayar fursunoni, da kawo karshen yakin, da janyewar sojojin Isra’ila daga zirin Gaza da shigar da kayan agajin jin kai.
A halin yanzu Hamas na tattaunawa a birnin Alkahira tare da masu shiga tsakani na Masar da Qatar.
Saidai, duk da haka, jami’in na Hamas ya caccaki Isra’ila saboda hana ci gaban da aka samu wajen tsagaita wuta.
A wani labarin kuma Akwai rahotannin da ke cewa Washington za ta yi matsin lamba kan gwamnatin Tel Aviv ta amince da wata sabuwar shawara kan tsagaita wuta a Gaza.
A ranar 18 ga watan Maris ne sojojin kasar Isra’ila suka kaddamar da wani harin ba-zata a zirin Gaza, inda suka kashe daruruwan mutane, tare da jikkata wasu da dama, tare da wargaza yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu, da yarjejeniyar musayar fursunoni.
A cewar ma’aikatar lafiya a Gaza, akalla Falasdinawa 50,983 aka kashe, akasari mata da kananan yara, tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila da
এছাড়াও পড়ুন:
Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza
Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi.
Shafin labarai na Isra’ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da matsaloli masu alaƙa da damuwa da kuma rasa abokai biyu a yaƙin na Gaza.
Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a BornoTRT ya ruwaito cewa an gano gawar sojan a cikin wani daji kusa da birnin Safed a arewacin Isra’ila bayan ya kasa samun sukuni da yadda zai yi ya magance damuwar da ya shiga.
“Ba zai iya jurewa ba kuma ya koka da ganin hotunan gawawwaki da kuma jin warin mutuwa a kullum,” in ji mahaifiyarsa.
A cewar kafafen yaɗa labarai na Isra’ila, adadin sojojin da suka kashe kansu ya ƙaru tun bayan ɓarkewar yakin Gaza a watan Oktoban 2023.
Wani rahoto daga jaridar Israel Hayom ya nuna cewa sojoji 21 sun kashe kansu a shekarar 2024.
A watan Mayu, jaridar Haaretz ta Isra’ila ta ce sojoji 42 sun kashe kansu tun bayan ɓarkewar yakin Gaza.
Duk da kiran duniya na tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza, inda ta kashe fiye da mutum 57,400, yawancinsu mata da yara, tun daga watan Oktoban 2023.